LABARAI

An Samu Nasarar Gano Yadda Gogarman Boko Haram, Kabiru Sakkwato Ya Nemi Yin Garkuwa Da ‘Ya’yan Kashim Shettima A Abuja

An Gano Yadda Gogarman Boko Haram, Kabiru Sakkwato Ya Nemi Yin Garkuwa Da ‘Ya’yan Kashim Shettima A Abuja

A wani shahararren labari da kamfanin jaridar The Cable ta wallafa a yau, Juma’a, 15 Ga Yuli, ta bayyana wani rahoton bayanan sirri kan yadda gogarman Boko Haram, Kabiru Sokoto ya yi yunƙurin sace ‘ya’yan Kashim Shettima a Abuja.

CHECK THIS OUT: Bidiyo Rigima ta barke bayan kama Shugaban ‘yan bindigar daji

 

Kabiru Umar Sokoto ya yi wannan yunƙurin ne wanda bai yi nasara ba a cikin watan Janairu, 2012, kamar yadda wasu bayanan tsaro na sirri su ka tabbatar. Ya nemi yin garkuwa da yaran ne lokacin da Shettima bai cika shekara ɗaya da zama Gwamna Jihar Barno ba.

Kabiru Sokoto dai shi ne gogarman da ya shirya harin bama-baman da Boko Haram su ka kai a Cocin St Theresa Catholic Church, a Madalla, kusa da Zuba a Jihar Neja. An rasa rayuka aƙalla 37 a harin, kuma mutane 57 sun ji munanan raunuka.

Da farko dai jami’an tsaro sun damƙe shi Gidan Saukar Gwamnan Jihar Barno da ke Asokoro, Abuja, a ranar 14 Ga Janairu, 2012, kafin a tsere daga hannun ‘yan sanda. An sake kama shi a Jihar Taraba bayan wata ɗaya, daga can aka maida shi Abuja.

A cikin wata takardar bayanan tsaro ta sirri da aka rubuta ranar Alhamis, 14 Ga Yuni, 2012, wadda sai kwanan nan bayanan sirrin cikin takardar su ka bayyana, Kabiru Sokoto ya yi nasarar shiga Gidan Saukar Gwamnan Jihar Barno da ke Abuja ne da niyyar sace ‘ya’yan Gwamna na lokacin, Kashim Shettima, wanda dama bai daɗe da ɗauke yaran daga Maiduguri ba, ya maida su Abuja saboda dalilai na tsaro.

Takardar bayanan na sirrin wadda aka aika ta Fadar Shugaban Ƙasa, ta na ɗauke da bayanin cewa kafin Kabiru ya nemi sace yaran a Abuja, an gargaɗi Shettima cewa Boko Haram na kitsa tuggun yadda za su yi garkuwa da ‘ya’yan sa domin su samu maƙudan kuɗaɗen biyan diyyar fansar yaran sa. Lokacin kuwa Shettima bai fi watanni takwas da zama Gwamnan Barno ba.

Shettima, wanda a yanzu shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, sai ya yanke shawarar kwashe ‘ya’yan sa daga Maiduguri zuwa Abuja. Yaran waɗanda biyu mata ne ɗaya kuma namiji, an maida wasu Turkish College a Wuse, ɗaya kuma British School a Gwarimpa.

KABIRU YA YI SHIGAR BAREBARI:

Rahoton bayanan sirri wanda wani babban jami’in tsaro ya sa wa hannu, ya yi zargin cewa Kabiru Sokoto ya yi shiga sanye da kaya irin na mutumin Barno. Ta haka ne ya samu damar shiga Gidan Saukar Gwamnan Barno, inda ‘ya’yan Shettima ke zaune a lokacin.

An bada rahoton cewa ya saɗaɗa ya shige cikin gidan a ƙarshen mako, a ranar 14 Ga Janairu, 2012, lokacin da babu cinkoso da yawa.

A wani yanayi na keta dokar tsaro, Kabiru ya roƙi wani baƙon da aka rigaya aka saukar a gidan cewa ya bar shi ya kwana a gidan, saboda shi ma baƙo ne, ba shi da masauki.

Baƙon wanda ba a bayyana kowane ne ba a cikin takardar bayanan sirrin, sai Ahmed Sanda, wanda a lokacin shi ne Babban Sakataren Kula da Gidan Saukar Gwamnan Barno a Asokoro, ya amince ya yi kwana ɗaya kacal.

YUNƘURIN YIN GARKUWA A KARƁI FANSAR NAIRA BILIYAN 1

Bayanan sirrin sun nuna cewa Kabiru ya yi niyyar yin garkuwa da yaran a ranar Litinin, 16 Ga Janairu, 2012, kan hanyar su ta tafiya makaranta.

Jami’an ‘yan sanda sun damƙe shi bayan ya kwana a Gidan Saukar Gwamnan Barno.

Shettima ya maida yaran waɗanda a cikin su babu wanda ya kai shekara 10 a lokacin zuwa Abuja, a cikin Disamba 2011, wato makonni biyu kafin yunƙurin yin garkuwa da su.

Ya ɗauke su daga Maiduguri zuwa Abuja bisa shawarar jami’an tsaro, kuma bayan an damƙe Kabiru Sokoto, an riƙa danganta cewa ba a rasa kusanci tsakanin wasun su da Boko Haram. An riƙa kuma tunanin cewa su na sanar wa Boko Haram ɗin bayanai a ɓoye.

An ce Boko Haram sun riƙa shirya yadda za su yi garkuwa da yaran domin su karɓi naira biliyan 1, wadda a lokacin kuɗin daidai su ke da dala miliyan 6.3.

JAMI’IN TSARO GUDA ƊAYA KAƊAI

Yaran sun bar gida Masaukin Gwamnan Barno zuwa makamata a ƙarƙashin kulawar antin su mata biyu, sai kuma wani kawun su ɗaya, yayin da mahaifiyar su kuwa ta na yawan zuwa Maiduguri ta koma Abuja ne, saboda ta na zama ofishin ta na Matar Gwamna a Maiduguri.

Rahoton tsaro na sirri ya nuna cewa an yi sakacin yadda aka haɗa yaran da jami’in tsaro ɗaya tal a kullum, wanda hakan ya sanya za su iya faɗawa tarkon masu garkuwa a sauƙaƙe.

Daga baya Shettima ya ƙara yawan jami’an tsaro a Gidan Gwamnatin Barno, sai ya ɗauke yaran ya maida su makarantun kwana.

Wani babban jami’in tsaro da The Cable ta tuntuɓa, ya ce ba shi da masaniya kan takarar bayanan sirri ta 2012, wadda ke ƙunshe da bayanin yadda aka yi yunƙurin yin garkuwa da yaran. Amma ya ce wannan zargin yunƙurin yin garkuwa da yaran, ya yi daidai da irin yadda Boko Haram ke shirya sace waɗanda su ke yin garkuwa da su.

Daga baya Shettima ya zama mutumin da Boko Haram ke so su ga sun kashe shi.

“Ban san da wannan takardar bayanan sirrin yadda aka kama Kabiru Sokoto a Gidan Saukar Gwamnan Barno ba. Daga baya Kabiru ya arce yayin da aka tafi da shi a binciki gidan sa. An sake kama shi daga baya.” Inji jami’in tsaron.

“An gayyaci wasu jami’an kula da Gidan Saukar Gwamnan Barno domin a yi masu tambayoyi. Tabbas an yi bincike kan yunƙurin ta’addanci a lokacin. Gaskiyar magana dai ba a same su da laifin komai ba. Kawai dai sakaci da aikin tsaro ne kawai, wanda kaɗan ya rage da lamarin ya yi muni. Da an same su da laifi ko abin ya yi muni kuwa, to da an gurfanar da su a kotu.

“Tuna lokacin Shugaba Goodluck Jonathan, ai babu kyakkyawar alaƙa tsakanin sa da Shettima. To da a ce a lokacin an samu wani laifi kan Shettima, to sai an fallasa shi ko a kai gulmar sa ga kafafen yaɗa labarai. Tunda gwamnan jam’iyyar adawa ne a lokacin.

“Wato kawai dai lamari ne na sakarcin da har za a yi sakaci wani ya shiga Gidan Saukar Gwamna, kai ko da shi gwamnan ma ba ya ciki a lokacin.”

A ranar 20 Ga Disamba, 2013 Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke wa Kabiru Sokoto ɗaurin rai-da-rai, saboda samun sa da laifin dasa bam a cocin Madalla.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please