Ansamu Nasarar kama Wasu ‘Yan Sakai Guda 2 Da Sunka Yi Ma Wata Matar Aure Fyade A Jahar Bauchi
An kama Wasu ‘Yan Banga 2 Sun Yi Ma Wata Matar Aure Fyade
‘Yan Sanda Sun Kama Wasu ‘Yan Banga Biyu Da Wata Matar Aure Aure suna yi mata fuade.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 30 ga watan Agusta.
An kama wasu ‘yan kungiyar ‘yan banga guda biyu bisa zargin aikata laifin damfarar wata matar aure a jihar Bauchi. Mutanen sun aikata laifin ne da bindiga a karamar hukumar Ningi da ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakili, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 30 ga watan Agusta, ya ce jami’an ‘yan sanda da ke Ningi sun kama wadanda ake zargin, Lawali Sule mai shekaru 30 da Babangida Shehu mai shekaru 30 a kauyen Dogon-ruwa, Rarraba.
“A ranar 25 ga wannan wata ta Agusta, 2022 da misalin karfe 2:00 na dare mutanen biyu suka hada baki a tsakaninsu inda suka kai farmaki gidan wani Alhaji Gare, dukkansu dauke da bindigogin hannu, sun shiga dakin matarsa Hadiza Alhaji (ba sunanta na gaskiya bane, mun sakaya) inda suka tambayi mijin nata tace ba ya gida.
Bayan haka suka yi mata barazana da bindiga da nufin su yi lalata da ita, kuma suka samu nasarar yin mata fyaden sakamakon firgicewar da ta yi da tsoro” in ji sanarwar.
An fara gudanar da bincike mai zurfi sosai akan lamarin, haka kuma an dauki ita matar da abin ya shafa zuwa babban asibitin Ningi don duba lafiyarta kuma likitoci sun tabbatar da faruwan lamarin”.
A yayin gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu bisa radin kansu.
An kwato Bindigogi daga hannun wadanda ake zargin, bindigogin Dane wato na toka guda biyu.
CP ya bayar da umarnin a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu.
Allah ya kare mana iyalanmu baki daya, Allah ka shiryar damu ka rufa asirinmu, ka sanya ma rayuwarmu albarka.
kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi