LABARAI

Jami’an Tsaro Sunsamu Nasarar Kama Wani Dan Jarida Da ake Zargi Da Hadakai Da ‘Yan Ta’adda


TUKUR MAMU YA SHIGA HANNU Labari ya tabbata gaskiya an kama fitaccen dan jarida Tukur Mamu wanda yake da alaka da Sheikh Dr Ahmad Gumi bisa zargin hada kai da ‘yan ta’adda

Tukur Mamu shine wanda ya shiga tsakanin ‘yan ta’adda da kuma ‘yan uwan wadanda akayi garkuwa da su a jirgin Kasa wanda ya kwaso fasinja daga Abuja zuwa Kaduna, Tukur Mamu yana da alaka ta aminci tsakaninsa da ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane, kuma duk sulhun da Sheikh Ahmad Gumi ya jagoranta da ‘yan bindiga tare dashi ake shiga jeji, shi yake hada rahoto

Bayan ya fuskanci barazana sosai daga hukumomin tsaron Nigeria, Tukur Mamu ya bayyana ajiye aikinsa na shiga tsakani da ‘yan ta’adda, ya bar Nigeria ya tafi Kasar Egypt tare da iyalansa inda daga nan zai wuce Kasar Saudiyyah sai hukumomin Egypt suka kamashi a can suka tsareshi

Yanzu haka ana kan hanyar dawo dashi Nigeria, Tukur Mamu ya daura alhakkin kamashi da akayi akan hukumomin Nigeria, kuma yace abinda aka tsara shine a tsareshi a wata Kasa ba Nigeria ba

Lamarin tsaro a Nigeria ya koma harkan neman kudi, zuwa yanzu ba mu da tabbaci tsakanin Tukur Mamu da masu iko da tsaron Nigeria waye maciyin amanar tsaro sai abinda ya biyo bayan bincike

Muna rokon Allah Ya mana maganin maciya amanar tsaron Nigera a duk inda suke

Source:Dattyassalafy

READ ALSO:  To Hanyar Zuba Mata Guba Acikin Lemu, Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Kawaye 3 Sun Kashe Kawarsu Har Lahira.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please