Kalli Yadda Rundunar Sojojin Nigeria Tasamu Nasarar Sambadar ‘Yan Bindigar Daji Takaida Sunyi Hijira Dole

Posted by

Kalli Yadda Rundunar Sojojin Nigeria Tasamu Nasarar Sambadar ‘Yan Bindigar Daji Takaida Sunyi Hijira Dole

Rundunar sojin Najeriya ta sake kai wani hari kan ‘yan kungiyar Boko Haram da ke ta’addanci a jihar Borno.

Janzakitv ta ruwqito daga Daily Post cewa sakamakon farmakin da sojojin da ke karkashin Operation Hadin Kai suka kaddamar kan wasu mayaqan, ya sanya da dama daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere daga kauyen Gaftari zuwa wani sabon wuri a Bazamri da ke kusa da karamar hukumar Konduga a jihar.

 

Kimanin ‘yan ta’adda 400 ne suka yi hijira tare da iyalansu bayan sun amince da kayen da sojoji suka yi masu inji sojojin.

Zaragoza Makama, kwararre a fannin yaki da ta’addanci, ya bayyana yadda ‘yan ta’addan Boko Haram su kusan 70 suka nutse a cikin kogi, bayan wani kazamin farmakin da sojoji suka kai a Gaftari da Shehuri, kauyuka biyu da ke tsakanin kananan hukumomin Bama da Konduga na jihar Borno.

‘Yan sa’o’i kadan bayan ‘yan ta’addan sun binne mambobinsu kusan 40 da suka mutu a nutsewar a lokacin da sojoji suka kai musu farmaki, an ce sun yi hijira zuwa wani sabon masauki tare da ‘yan uwansu.

Wata majiya da ta zanta da jaridar Daily Post ta ce, “Sun tafi tare da iyalansu, wadanda adadinsu ya kai 400, bayan sun yarda cewa sojojin Najeriya sun fatattake su.

Allah ya kara dafa ma sojojin Najeriya akan yaki da ta’addanci baki dayansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *