Ministan Sadarwa Pantami ya gwangwaje jarumi Nuhu Abdullahi da babban mukami a hukumar NIMC

Posted by

Ministan Sadarwa Pantami ya gwangwaje jarumi Nuhu Abdullahi da babban mukami a hukumar NIMC

Ministan sadarwa, Farfesa Aliyu Isa Pantami, ya gwangwaje jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da babban mukami a ma’aikatarsa kamar yadda shafin Kannywood Celebrities su ka bayyana.

Kamar yadda su ka wallafa wata takarda mai dauke da tambarin masana’antar sadarwa, an nuna yadda Ministan ya bai wa jarumin mukamin jakadan ranar NIMC da za ayi ta shekarar 2022/2023.

Kamar yadda takardar ta nuna, dalilin ranar shi ne wayar da kan jama’a dangane da hakkinsu, ayyuka da damar su a tattalin arzikin kasa.

Kuma hakan dama ce wacce za ta nuna ayyukan gwamnati karara dangane da NIMC. Mukamin na shekara daya ne cur kuma zai fara aiki ne a ranar 16 ga watan Satumban 2022 zuwa ranar 15 ga watan Satumban 2023.

Za a iya sabunta nadinsa amma sai an ga yanayin kwazonsa a aikin. Har ila yau, ma’aikatar NIMC za ta iya lokaci bayan lokaci gayyatarsa don wayar da kansa dangane da harkar lambar katin dan kasa da kuma harkoki masu kama da hakan da sauransu.

Mu na taya jarumin murna da fatan Allah ya taya shi riko. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *