Shahararren Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Da Ya Addabi Mutane Ya Ajiye Makamai Ya Ce A Zauna Lafiya
Shahararren Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Da Ya Addabi Mutane Ya Ajiye Makamai Ya Ce A Zauna Lafiya.
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, ya yaba da matakin da Turji ya dauka na gujewa ‘yan bindiga ya kawo zaman lafiya a kananan hukumomi uku da ke fama da munanan hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Ya ce, a cikin makonni biyar da suka gabata, ba a samu wani tashin hankali tsakanin Hausawa da Fulani a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji na jihar ba, saboda tattaunawa dake wakana a tsakanin bangarorin biyu.
A cikin rahoton wanda gidan Talabijin na Channels ya fitar, ya ce kwamitin da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kafa, ya gana da sansanonin ‘yan bindiga tara a jihar, inda suka samu jin ta bakin ‘yan fashin.
Da yake jawabi, ya ce a yanzu Turji na hada kai da gwamnatin jihar domin ganin an kawo karshen ‘yan fashi a jihar, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zamfara.
Rahoton da ke cewa sarkin ‘yan fashin, Bello Turji, ya rungumi zaman lafiya, ya jawo cece-kuce daga jama’a.
Me zaku ce akan wannan? Ku Saki Jikinku wajen fadin ra’ayoyin ku tare da mu a wannan shafi
https://youtu.be/SHpwmTxDUng