Tarar Naira Miliyan 1 da ɗaurin Wata 6 shine Hukuncin duk wanda yace zai aure ta Indai ta amince

Posted by

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ƙiyasta cewa a Nigeria akwai mutane masu buƙata ta musamman da adadin su yakai kimanin Miliyan 25, kusan Kashi 20 kenan (20%) na al’ummar Nigeria.

Me ake nufi da Mutane Masu buƙata ta Musamman ?

Mutane Masu buƙata ta musamman ko kuma “Person with Disability” Sune mutanen da suke da wata matsala ta zahiri ko ta ɓoye wacce zata hana masu aiwatar da ayyukan su na yau da kullum kamar yadda kowa yake yi. Duba Sashi na 57 (a)(b) Na The Discrimination Against Persons with Disabilities (Prohibition) Act, 2018.

Dalilin yin wannan rubutu shine: Jiya akwai Video da Hotunan wannan baiwar Allah Fatimah (Wacce na saka hoton ta) da suka yita yawo a kafafen Sada zumunta na zamani bisa wata Jarabawar da Allah ya Jarabceta da ita, muna mata addu’ar Allah ya bata lafiya kana kuma yasa taci Jarabawar, Ameeen.
Saidai daga lokacin da hotunan da Videon nata suka fara yawo mutane da dama sun yita turawa da saƙunan da yake cewa: “Su wallahi Indai zata aure su to su sun yarda zasu aure ta”
Wannan magana da suke yayatawa laifi ne a dokar ƙasa domin kuwa Discrimination ne, Idan muka duba Sashi na 42 na Kundin tsarin Mulkin Nigeria za muga ya haramta a tsangwami mutum saboda addinin sa ko aƙidar ko kuma ƙabilar sa, saidai baiyi bayani akan tsangwamar da ake yima mutane masu buƙata ta musamman ba, haka ne yasa Majalisar Ƙasa tayi wani kundin doka mai suna “The Discrimination against Persons with Disabilities (Prohibition) Act, 2018” doka ne da aka yita domin ta kare martaba da ƙimar duk wani mutum mai buƙata ta musamman.

Mu duba wannan kundin a cikin Sashi na 1(1) na DAPD, Act 2018 za muga ya bayyana cewa: haramun ne ka tsangwami duk wani mutumin da yake da wata buƙata ta musamman. Don haka idan muka matsa gaba a Sashi na 57 na Wannan Kundin za muga ya bayyana cewa Discrimination anan tana nufin kayi treating ɗin mutumin (Wato kayi masa mu’amala daban da yadda zaka yima wanda ba yada wata buƙata ta musamman) kuma ya zama ka yimasa mu’amalar ne saboda wannan Disability din da yake da, so idan muka kalli lamarin wannan baiwar Allah daga lokacin da wannan jarabawa ta sameta kowanne mutum da wanda ya kamata da wanda bai kamata ba, da wanda ko kallo ma bai isheta ba wai yau sune suke ta aiko mata da saƙon cewa wai zasu aureta Indai har ta yarda tana son su, tabbas sunyi mata hakane saboda wannan jarabtar da suka ga ta sameta, don kuwa ba aure tace masu zatayi ba, ba rasa mijin aure tace masu tayi ba, ba shelar neman miji tayi ba, haka kawai, don haka duk wanda ya turo mata wannan saƙon ya aikata laifin Discrimination, domin waɗannan saƙonnin zasu sare mata gwiwa ne, inda zata riƙa kallon kanta kamar ba cikakkiyar mutum ba, zata riƙa jin cewa yanzu ita Shikenan duk wani tsari da burin ta na rayuwa ya rushe tunda gashi har waɗanda ko kallo ma basu isheta ba wai yau sune da cewa wai “ZASU IYA AUREN TA”

Sashi na 30 na DAPD Act, 2018 Cewa yayi lallai ne mu ƙarfafa gwiwar duk wani mutumin da yake da buƙata ta Musamman, a abinda ya shafi “Public Life” yanzu Fisabilillahi waɗannan masu yayata cewa wai su zasu iya auren ta shin ƙarfafa mata gwiwa suke yi, ko kuma sare mata gwiwa !

To duk wanda ya aiko mata da wannan nonsense and idiotical message ya aikata laifi a dokar ƙasa kuma zata iya kai ƙarar shi kotu, a tilasta masa biyanta diyyar kuɗi Naira Dubu ɗari (₦100,000.00) ko kuma a ɗaure shi na tsawon wata 6, ko kuma a haɗa masa duka biyun, idan kuma Artificial Person ne ya aikata wannan laifin zai biya ta tarar Kuɗi ne Naira Miliyan ɗaya cas, (₦1,000,000.00) Duba Sashi na 1(2)(a)(b) na DAPD Act, 2018.

Kazalika, bayan wannan kuma zata iya ƙarar mutum akan cewa ya haifar mata da Emotional and Psychological Pain, don haka anan ma ya aikata laifi zai fuskanci hukuncin ɗauri gidan kaso na Shekara ɗaya, sannan kuma zai biya ta tarar Kuɗi Naira dubu ɗari biyu (₦200,000.00) duba Sashi Na 14 na VAPP Act, 2017.

Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
22nd August, 2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *