KANNYWOOD

Tirkashi Ni Ba Dan Maula Bane Jarumi Baba Ari Ya Saki Zazzafan Martani

Barkadawannan lokaci muna Murnar shigowa shfinmu na KuryaLoaded.ng dakunkayi  yau munzomaku da wata fira da mujallar film tayi da

tsohon jarumi amasana’antar shirya fina finai ta kannywood dake a arewacin Nigerian waton Jarumi Aminu Ari Wanda akafi sani da Baba Ari

JARUMIN barkwanci a finafinan Kannywood, Aminu Baba Ari, ya bayyana cewa shi fa ba ɗan maula ba ne a cikin harkar fim, domin ban da fim ya na da harkokin sa na kasuwanci da ya ke yi.

Jarumin ya bayyana haka ne a lokacin da mujallar Fim ta tattauna da shi a game da irin yabon wasu da ya ke yi a cikin fim, musamman manyan mutune ko masu kuɗi, wanda hakan ya sa ake ganin wani salon maula ne kawai ya ke yi.

Baba Ari ya ce, “Ni fa ba ɗan maula ba ne. Kama sunan mutane da na ke yi ba don su na ba ni kuɗi ba ko don su ba ni na ke yi, domin na san ko a baya da na ke faɗar sunan Matawallen Maradun sai da aka daina kira na a saka ni a fim.”
Ya ƙara da cewa: “Duk irin waɗannan abubuwa abu ne na hassada, don haka duk abin da za ka yi idan mutum ya na ƙin ka, ko ruwa ka faɗa sai ya ce ka tayar masa da ƙura.

“Don haka ni a gani na don na faɗi mutum a fim ba laifi ba ne. Kamar a yanzu, misali, don na kama sunan mutum to na ce ya ba ni kuɗi ne? Ai ba roƙo na yi ba. Idan har roƙon zan yi ba sai an gayyace ni a fim zan shigar da roƙon ba.

“Amma dai ni a gani na duk wanda ya ji an faɗi sunan sa a fim zai ga an mutunta shi, an daraja shi. To, waɗanda ba sa so sai su ga kamar an zage su. Ka san ni kuma ba na zagi, sai dai baƙar magana, ta na nan da yawa a kai na.”

Ɗan wasan ya yi kira ga mutane da su yi masa kyakkyawar fahimta, amma kuma ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya taka shi, to ba ya barin sai ta kwana.

Tau Maikaratu mezakace akan wannan labarin kuyimuna comments na ra’ayoyinku a sashenyin comment dake a kasan wannan video. Mungode

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please