Wadannan Photunan Na Tinubu Sun Janyo Masa Tsokana Da Cece Kuce a Social Media Fiye Da Tsammani

Posted by

Akwann Nan ne Aka Saki wasu Biyo Da Photunan Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyar Apc Wato Bola Ahmed Tinubu Akan Keke. Motsa jiki anman kuma bayan sallafa wadannan Photunan

sai suka zama abin tsokana da qaryatawa a kafafen Sadarda Zumunta indo kowa yake rofa albarkacin bakinsa  dagaciki ga abinda wani Marubucin Facebook Ya Ce Wato Dattyassalafy

SUN FARA BOYE GASKIYA TUN DAGA YANZU

Jiya cabals a gidan siyasar Kaka Tinubu sun fitar da wani gajeran bidiyo a shafinsa na Facebook wanda bai wuce second 6 ba suka nuna Tinubu akan keken motsa jiki irin na marassa lafiya da ake ajiyewa a Asibiti

A cikin bidiyon, sun karyata labarin cewa Tinubu ya rigamu gidan gaskiya a Asibitin da yake jinya a London, sunce bai janye daga takaran shugaban Kasa ba wai ya warware gashi nan ma yana motsa jiki, kuma ya shiryar zai shugabanci Nigeria

Abu na farko, menene abin boye gaskiya game da rashin lafiyar mutum? kowani bil’adama yana rashin lafiya, kuma kowa zai mutu idan kwanansa ya kare

Kuma me yasa bidiyon suka daukeshi second 6 kacal? kamata yayi suyi bidiyo na minti 10 yana motsa jiki, sannan duk wanda ya kure wa bidiyon ido da kyau akayi zooming dinsa za’a ga alamar tambarin asibiti, Likititocin Physiotherapist suna yiwa wadanda suke fama da jinyar Paralysis irin wannan dabi’ah na motsa jiki

Tinubu yayi tsufan da ba zai taba iya rike Nigeria ba, akwai wanda idan tsufa yayi tsufa za’a ga yana karkarwa kamar yadda wannan yake yi, tsufansa da rashin lafiyarsa a bayyane suke, amma karfi da yaji suna son su boye gaskiya saboda su daura mana marar lafiya domin su cigaba da cin amanar da suka saba

Abu mafi muhimmanci ga rayuwar Tinubu shine a kaddamar da takaran shugaban Kasa yana nan, amma jam’iyyar APC ta dage saboda dan takaranta yana jinya a Asibiti

Kwamitin zaman lafiya na ‘yan takaran shugaban Kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban Kasa Abdussalam Abubakar ya jagoranci zama da dukkan ‘yan takaran shugaban Kasa domin su sanya hannu, kowa yazo ya sanya hannu amma banda Tinubu saboda lalura na rashin lafiya, inda kalau yake babu abinda zai hanashi zuwa ya sanya hannu

Kaciya da zafi, an shamu mun warke ba za’a kuma ba, yaudaran da aka mana ya isa haka, ba zamu bari ku sake yaudaran mu ba Insha Allah

Kaka Tinubu اللهم يشفيك

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *