‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Jami’an Tsaro Da Mutanen Gari Masu Yawa A Jihar Katsina

Posted by

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda da dama tare da mutanan gari wanda ba suji ba basu gani ba, a yankin kauyukan jihar Katsina da cikin garin jihar a ranar laraba.

A Daren Jiya ‘yan Bindiga Suka Kai Hari A Garin Gatigawa Dake Karamar Hukumar Kankara A Jihar Katsina Inda Suka Kashe Jami’an Ƴan Sanda Biyar Da Kuma Kashe Mutanen Gari Uku Har Lahira Da Raunata Mutane Da Dama.

Majiyar shafin Janzakitv, Ta samu ganawa da wani mutum daya kasance Shaidar gani da ido Cewa Ƴan Bindigar Sun Shigo Garin ne, na gatigawa Da Misalin Karfe 5:40 Na Yammacin Laraba Bisa Babura Sama Da Dari Uku da hamsin tare Da Manyan Bindigogi na musamman a lokacin.

Kuma Sun Kashe Ƴan sanda sama da mutum hamsin yayin da suka hada da mutanan gari da dama takan mai uwa da wabi, ma’ana wanda kwanan sa, ya kare a wannan lokacin da Mutanan suka kai musu farmakin a kauyen nasu.

Hakika batun yanzu irin wannan Abubuwan suke faruwa ba a cikin jihar ta katsina da kauyukan dake kewaye da jihar koda yaushe suna fama da hare – haren na ‘yan bindiga musamman a kauyukan jihar na katsina.

Gwamnatin jihar katsina karkashin jagorancin mai girma Gwamna Aminu Bello Masari, tayi sanarwa cewa da yardar allah zasu tsaurara bincike na musamman da Jami’an tsaron dake aiki a jihar nan bada jimawa ba.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *