LABARAI

Abin Haushi Da Takaici Yadda Dattijo Dan Shekara 70 A Duniya Ya Yiwa Yarinya Yar Shekara Bakwai Fyade A Bauchi.

Dattijo Dan Shekara 70 A Duniya Ya Yiwa Yarinya Yar Shekara Bakwai Fyade A Bauchi.

Jami’an ‘yan sanda a hedikwatar ‘yan sandan Najeriya shiyya ta 12 da ke Bauchi sun kama wani dattijo mai shekaru 70, Alhaji Umaru Daura da ake zargi da lalata da ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara bakwai.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan shiyyar (ZPPRO), SP Thomas Goni, wadda aka raba wa manema labaru kwafin a Bauchi ranar Talata.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne kwanan nan a kauyen Kawo Rauta da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

ZPPRO ya ci gaba da cewa mahaifin wadda aka yiwa fyaden, Alhaji Habu, ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, yana mai cewa, “An kama wanda ake zargin da hannu da hannu dumu-dumu yana lalata diya ta mai shekaru bakwai.”

Thomas Goni ya kara da cewa, mataimakin babban sufeton ‘yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta 12 a Bauchi, AIG Audu A. Madaki, ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.

Jaridar Sokoto

Source:Katsina Online 

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please