LABARAI

Ankama Wani Matashi Bayan Yayiwa Matar Mai Gidanshi Fyade

Ankama Wani Matashi Bayan Yayiwa Matar Mai Gidanshi Fyade

Wani matashi dan shekaru 20 ya yiwa matar ubangidansa fyade a jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Jume Bello da laifin yiwa matar uban gidansa da wasu mata biyu fyade a kauyen Jikamshi da ke karamar hukumar Musawa

Da yake gabatar da wanda ya yi fyaden tare da wasu masu laifin a gaban manema labarai a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP Gambo Isah, ya ce wanda ake zargin bayan ya samu nasarar aikata mummunar aika-aika ‘zina’ da matan, ya kuma sace musu kudi da sauran kayayyaki.

SP Gambo Isa ya kuma kara da cewa, “a ranar 31 ga Mayu, 2022, da misalin karfe 9:00 na dare, wadanda abin ya shafa ‘yan shekara 18 zuwa 25, dukkansu a kauyen Jikamshi, sun kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na Musawa cewa a ranaku da lokaci daban-daban, wani Jume Bello mai shekaru 20 da abokan aikinsa sun shiga gidajensu sun kai musu hari da wuka, suka yi musu barazana, inda suka kwace masu abubuwanda da suka hada da kudadensu, wayar hannu, da kuma tilasta musu suka keta masu haddi.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please