LABARAI

Jami’ai Sun Samu Nasarar Kama Wani Matashi Da Yaje Fadar Gwamnatin Jihar Katsina Da Yunkurin Kashe Gwamna Masari Duba Abinda Ya Faru

Jami’ai Sun Samu Nasarar Kama Wani Matashi Da Yaje Fadar Gwamnatin Jihar Katsina Da Yunkurin Kashe Gwamna Masari Duba Abinda Ya Faru

Wata majiya mai qarfi tamu tasamu labarin cewar Jami’an tsaro na Yan Sanda Ajihar Katsina Sun Samu Nasarar Kama Wani Matashi A bakin kofar gidan gwamnatin jihar

dayunkurin Kashe Mai girma gwamnan Jihar Kaman Yanda Mukasamu A Shafin JanzakiTv Sun Wallafa

Sabon labari Wani matashi Yaje Fadar Gwamnatin Katsina Da Tabarya Domin Daukar Fansar Mahaifiyarsa Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe.

A jiya Alhamis ne wani ya shiga gidan gwamnatin Katsina da tabarya da nufin ya zo daukar fansa akan kisan da wasu mutane sukayi wa Mahaifiyarsa.

Shafin Janzakitv, ya samu labarin cewa” sai da matashin ya shiga har cikin fadar gwamnatin kafin jami’an tsaro dake bakin kofa su ankara dashi a wannan lokaci.

Bayan sun kama matashin ne, suka lakada masa dan banzan dukan tsiya sakamakon taurin kan daya nuna musu kafin daga bisani su tambaye shi dalilin zuwan sa.

Jami’an tsaron sun tambayi matashin dallilin daya saka ya shiga har cikin fadar gwamnatin jihar da zummar, daukar fansa akan gwamna masari.

Yayin da yake bayyana cewa” wasu mutane sun shiga har cikin gidan su, sun kashe masu mahaifiya sannan kuma ya shigar da kara amma babu wani bayani akan magana.

Hakan ya fusata shi har takai ga yaje fadar gwamnatin domin ya isarwa da gwamnatin wannan sako ko zata duba lamarin nasa ta wannan hanya a cewar matashin.

Kuci gaba da kasancewa da shafin Janzakitv, gidan labaran duniya kowace rana mungode masoya shafin mu kuci gaba da bibiyar mu Janzakitv, naku ne, mungode.

READ ALSO:  Sani Sadiq Fitaccen Jarumin Kannywood The phrase "Yayi murnar cika shekara 9 da Aure matarsa Murja inda allah" is used.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please