Innalilahi wainna ilaihir raji’un Bayan yasamu karaya uku sakamakon gidan da yafado a kasuwar beirut yau Allah yayi masa Rasuwa

Posted by


Bayan yasamu karaya uku sakamakon gidan da yafado a kasuwar beirut yau Allah yayi masa Rasuwa.

Kamamar Yadda kuka sani acikin wannan satin ne

Wani gini mai hawa uku ya ruguje a wata shahararriyar kasuwar waya da ke Titin Beirut a jihar Kano a yau Talata.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana a lokacin da ginin ya ruguje kan ‘yan kasuwa da masu sayar da abinci da sauran mutane a kasuwar.

A cewar shaidun gani da ido da suka zanta da wakilin Daily Nigerian Hausa, sun ce a halin yanzu mutane da dama sun maƙale a cikin ɓaraguzan ginin.

Wani shaidar gani da ido ya ce an fito mutane uku da ransu amma da yawa suna makale a cikin baraguzan ginin.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ana ci gaba da aikin ceto.

Ƙarin bayani na nan tafe…

Muna samun wannan rahoto
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun , Allah yayiwa dan uwa Danladi rasuwa yau , wanda yayi karaya ukku asanadiyya ibtila’e dayafaru a kasuwarmu ta beirut , zaayi jana’izarsa a Rimin Kebe Gidan Dakin layin Mal Kabiru.
Damisalin karfe 3:pm
Allah yajikansa yasa aljannace makoma

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *