LABARAI

Tirkashi A Jiya An Nada Wani Qasurgumin dan ta’adda Sarauta a Zamfara

Zamfara- An yi wa rikakken dan ta’adda Ado Aleru, nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar Yandoton daji dake jihar Zamfara.

Yandoton daji tana daya daga cikin sabbin masarautu biyun da gwamnatin jihar Zamfara ta kirkiro a watan Mayun da ya gabata.

An kirkiro ta ne daga masarautar Tsafe. Sabon sarkin Yandoton Daji shine Aliyu Marafa.

Hukuncin bai wa shugaban ‘yan bindigan
sarauta ya biyo baya ne sakamakon kokarin da yayi na tabbatar da zaman lafiya tare da jagorantar yarjejeniya tsakanin masarautar da yan ta’addan da suka addabi karamar hukumar Tsafe.

An yi nadin sarautar a fadar masarauta Yandoton Daji kuma shugaban masarautar karamar hukumar Tsafe da kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida, DIG Ibrahim Mamman Tsafe duk sun samu halarta.

Shugaban ‘yan bindigan shi ne ya jagoranci farmakin da aka kai Kadisau, wani yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina inda aka halaka kusan mutum 52.

Rundunar yan sandan jihar Katsina a 2019 ta bayyana cewa tana nemansa ido rufe inda ta saka N5 miliyan ga duk wanda ya kawo shi.

Yankuna masu yawa a fadin jihar sun fada halin haula’i sakamakon farmakin ‘yan bindiga da suke kai samame kauyuka, su sace shanu tare da sace mutane domin karbar kudin fansa.

A 2019, gwamnatin jihar ta yi yarjejeniyar zaman lafiya da yan bindiga. Kusan sabbin motoci kirar Hilux 15 da kudi tsagwaro aka bai wa tubabbun yan bindiga a 2020, Sahara Reporters ta ruwaito.

Innalillahi Wa’Inna’ilaihi Raji’un Allah Yayiwa Babban Jarumin Cikin Masana’antar Kannywood Ali Artwork
Duk da wadannan yarjejeniyar, yankunan jihar suna cigaba da samun farmaki inda ake sace mutane tare da halaka su.

masu sauraranmu a koda yaushe bayan wannan labarin ya riskeku zamu so karbe ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci sannan muna da bukatar da ku danna mana alamar kararrawar sanarwa.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please