Innalillahi Kwanan Nan Jaruma Fati Bararoji Ta Bayyana Irin Matsananciyar Cutar Dake Damunta

Posted by

TUN a safiyar yau Asabar aka fara yaɗa waɗansu hotuna a aoshiyal midiya na jarumar Kannywood Fati Baffa Fagge (Bararoji) waɗanda su ka nuna Fatin ta yi wata irin ramewa.

Ganin hotunan, sai mutane su ka dinga surutu a kan ko dai tsohuwar jarumar ta yi rashin lafiya ne? Idan haka ne kuma, wace irin cuta ce ke damun ta?

Binciken mujallar Fim ya nuna cewa asali dai hotunan sun fara bayyana ne a shafin ita jarumar na TikTok da ‘status’, daga nan su ka yaɗu zuwa sauran wasu shafukan na soshiyal midiya.

Mujallar Fim ta kira Bararoji ɗin a waya domin tabbatar da halin da ta ke ciki. Mun tambaye ta ko ta na da masaniya kan surutun da ya ɓarke game da ita a soshiyal midiya.

Fati ta amsa da cewa: “Gaskiya na yi mamaki da na ji mutane su na ta surutu a kan wannan hotunan, har ma ake cewa ba ni da lafiya. To ni lafiya ta ƙalau, ban yi rashin lafiya ba.

“Abin dai da na sani cikin satin nan na yi tafiya zuwa Abuja, daga nan sai na wuce Sokoto wajen taron biki, kuma ban huta ba na dawo Kano. To wannan yanayi na tafiyar ya sa ni gajiya, duk ido na su ka faɗa, kuma na zo na yi hotunan a haka, shi ya sa ake ganin kamar ba ni da lafiya ko na yi wata rashin lafiya.

“To gaskiya lafiya ta ƙalau, kawai dai gajiyar tafiya ce.”

Faƙat, Fati Bararoji! Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana, amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *