Wata sabuwa Nafisat Abdullahi tasaka naira dubu dari (N100,000) akan akawo mata wasu hotuna sabida rikicinsu da naziru sarkin waka

Posted by

hausa ta Kannywood Nafisat Abdullahi ta sanya kudi har naira dubu dari kan wadda ya iya gano wata wacce aketa wallafa hotunanta da sunan cewar Nafisat ce.

Idan baku manta badai jaruma Nafisat Abdullahi tafito tayi wata magana akan cewar baikamata iyaye sudinga haifan ya’yan da bazasu iya kula dasu ba, wanda hakan ya janyowa jarumar zagi dacin mutunci, inda wasu kuma suke ganin cewar abinda jarumar tafada gaskiyane.

 

 

Wanda mawaki naziru sarkin waka shima yafito yayi magana, inda yake fadin cewar bawai iya almajirai bane wanda iyayensu basa iya rikesu, idan mutum yana neman wanda iyayensu basa kula dasu to yazo masana’antar film.

Hakan ya matukar janyo cece kuce musamman a shafin twitter, inda mutane sukaita wallafa wasu hotuna tareda cewar Nafisat ce inda suke fadin cewa (indai haka yar film take gwanda su haifi almajirai 10).

Saidai jarumar tafito ta kare kanta inda take fadin cewar ba ita bace acikin wannan hotunan da mutane suke wallafa, inda jarumar tace tasaka kudi naira dubu dari (N100,000) ga duk wanda ya fada mata asalin sunan shafin yarinyar da ake wallafa hotonta da sunan cewar Nafisat Abdullahi ce.

Nafisat Abdullahi

Hakan da jarumar takesonyi dai baya rasa nasaba da tanason fahimtar da mutane cewar tabbas ba ita bace acikin hoton, tanaso idan aka nemo Mata waccar wanda take hoton mutane su sake gasgata zancenta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *