Jaruma Nafeesat Abdullahi Tamusanta Cewar Kallon Fina finan Hausa Na Lalata Tarbiya

Posted by

Fina finan Hausa Basu Lalata tarbiya saidai in daman yaranku Marar Tarbiya Ne

Muna matuqar farincikin ziyartar wannna shafin na KuryaLoaded dakunkayi kamar yanda munkasaba kawomaku sahihan labaran duniya da na Kannywood Acikin harshen Turanci dana hausa ayau

Munsamu wani rubutuda shafin jaridar a idonmikiya da sunkayi inda sunkace shahararriyar jarumar shirya fina finan hausa ta kannywood wato jaruma Nafeesa abdullahi tace fina finan hausa basa lalata tarbiya saidai inhar daman yaranku basuda ita ga rubutun kamar haka

Ko Kaɗan Finafinan Hausa Basa Ɓata Tarbiyya Sai Dai In Dama Can Yaranku Basu Da Tarbiyya A Gida, Nafisat Abdullahi Ta Caccaki Masu Sukar Finafinan Hausa

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar finafinan Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kalamai masu kaushi akan mutanen dake sukar finafinan Hausa.

Nafisa Abdullahi a wani rubutu da tayi a shafin ta na Twitter tace ko kaɗan finafinan Hausa ba sa ɓata tarbiyyar yara sai dai idan dama can asali yaran ba su samu tarbiyya a gida ba.
“Ba yadda za a yi mutane su bar yaran su na kallon finanfinan ƙasar Amurka (Hollywood), finafinan Indiya (Bollywood) dana kudancin Najeriya (Nollywood), sannan su buɗe baki suce finafinan Hausa ne ke ɓata tarbiyyarsu.” Inji ta

Mutane da dama dai na ganin cewa finafinan Hausa na wannan zamanin na zama wani abin gurɓata tarbiyyar yara, musamman yadda ake nuna wasu abubuwan da suka ci karo da al’adar Hausawa.

An sha korafi akan yadda masana’antar ta koma nuna wasu abubuwa waɗanda suka ci karo da ɗabi’a da al’adar Hausawa, sai dai jarumar na ganin cewa masana’antar bata ɓata tarbiyya.

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *