Kasar Pakistan Nacikin Bala’in Ambaliyar Ruwan Sama Da Iska Hadi Da Girgizar Kasa Anrasa Rayukka Da Gidaje Fiyeda Miliyan 30

Posted by

Halin da ‘kasar Pakistan ta samu kanta a ciki shekaran jiya

Jarabawar da kasar Pakistan ta fada ciki abun tsoro ne, abun ka zubar da wahaye kayi kuka ne, na ambaliyar ruwa da girgizar kasa Mai muni da ya faru a kasar shekaran jiya Litinin, duk Wanda yayi ido biyu da videos din abubuwan da suka faru wallahi ko bai yi kuka da idon sa ba sai yayi kuka zuciya.

~ Iska ce ta kada, tabi ta kan kasar dauke da ruwan sama Mai tsananin karfi, Wanda ya Kai ga hatta duwatsu suna ballewa daga cikin kasa suna markade mutane😭.

Har yanzu ba’a san yawan mutanen da suka mutu ba, domin har zuwa yau Laraba da muke magana lamarin bai sassauta ba.
~ Kana gani iska tana rushe gidajen da daruruwan mutane suna ciki, kana jiyo ihun mutane da kururuwar su suna halaka. Zuwa yanzu dai an iya kiyasta bacewar mutane Miliyan 30 da ruwan ya tafi dasu ko ya tafi da gidajen su.

Bala’in da afkawa kasar Allah kadai yasan girman ta da fadin ta, ruwa ya tafi da gidaje, Gadoji, hanyoyi, Tituna, mutane, dabbobi gonaki da kasuwanni.

Tun a cikin watan June da July Pakistan ta fara fuskantar wannan matsalar, Amma na shekaran jiya yayi muni, kuma ya jijjiga miliyoyin mutane a fadin duniya.

~ Kasar Pakistan kasa ce ta zallan Musulmi, masu ilimin Kimiyya da kwarewa a bangarori daban daban na rayuwa.
Har yanzu manyan kasashen duniya basu yi wata magana ko bayar da taimako ma kasar ba, wasu kasashen Musulmai ne kadai suka Dan fara nuna zasu taimaka, sai kungiyar shugabanni Musulmi na duniya.

~ Naga wani videon wani mutum da duwatsu sun fasa shi, kansa ya fashe, kwakwalwar sa ta zubo kasa Amma bai mutu ba yana magana, yana wasiyya, Kuma a take ya cika.

Naji dadi kwarai da naga shugaban kasa Buhari yana daga cikin wadanda suka fara bayyana cewa Nigeria zata taimaki kasar Pakistan akan wannan jarabawar.

Akwai gidajen da duk mutanen gidan sun mutu, babu Wanda yayi saura, akwai garuruwan da kamar duk an shafe su ne, ruwa ya tafi dasu, masallatai duk sun rushe.

~ Zaka gari kamar Kano Amma da kyar ka samu abinda zaka ci, saboda ruwa ya tafi da komai, tun ana ciro mutanen da ruwa yake wucewa dasu har an gaji an daina, zaka ga ruwa ya dauko mutum, mutane suna kuka suna ihun neman tsira Amma babu Wanda zai iya ciro su, idan kaje kaima ruwan zai ja ka, ya tafi da kai, Laa ilaha illal Lah 😭.

Jama’a wallahi bamu fi karfin Allah, Pakistan tana cikin tashin hankali.
Mutane sun shafe kwana uku basu ci komai ba, Yara suna mutuwa, ruwa yana Kara sauka, iska tana kadawa da jijjiga kasa.
~ Allah kawo sauki da mafita, Allah ka tsare mu ba dan halin mu ba.🤲

kalli Photunan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *