Yadda Wani Ango Ya Auri babbar Qawar Matarda Zai Aura Ana gaf Da biki

Posted by

Yadda Wani Ango Ya Auri babbar Qawar Matarda Zai Aura Ana gaf Da biki

Bismillahirahmanin rahim Aminci allah ya tabbata gareku ina maku bark da zitartar wannan shafin na KuryaLoaded

Kamar kullum yanda shafin namu ya ke kawomaku sahihan labarai acikin harshen hausa yauma munzo maku da wani labarin

Ango Yayi Wuff Da Babbar Kawar Amarya a Ranar Daurin Aure Bayan Amarya Tayi Masa Cikas

Majiyarmu tasamu wannan labarin ne a shafin yanargizo na Arewatimes Inda suka ruwaito labarin kamar haka

A wani labari da muke samu ya shiada mana cewa al’ummar garin Mararraban Guruku da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nassarawa sun wayi gari da abin mamaki a ranar Asabar da ta gabata bayan wata budurwa mai suna Hafsat Danladi ta bukaci a dakatar da daurin aurenta da wani saurayi.

Sai dai ana cikin haka sai daya daga cikin kawayenta da suka zo gidan bikin mai suna Zainab Sa’id ta gabatar da kanta ga saurayin tare da bukatar a yi auren da ita

Mun samu labarin cewa daurin auren wanda da farko aka yi niyyar yi bayan Sallar Azahar, an bukaci jama’a su yi hakuri su sake komawa masallaci bayan Sallar la’asar, inda aka daura auren a lokacin bayan an tuntubi waliyyan sabuwar amaryar da kuma yi mata gwaje-gwajen kiwon lafiya.

Wani abokin angon mai suna Ibrahim Idris, ya shaida wa Aminiya cewa angon Sulaiman Musa ya suma, amma bayan farfadowarsa sai aka sanar da shi cewa da Zainab za a yi auren a yanzu.

“An gabatar da ita a gare shi, nan take ya ce ya amince. Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda tsohuwar budurwar ta saki jiki ta fadi bayan samun labarin daura auren da wata,” inji shi.

Kuma Amihad.com ta samu labarin ta yi yini biyu kwance a asibiti. Bikin ya yi armashi sosai fiye da yadda aka tsara yi da farko, sannan angon ya samu tarin kyaututtuka.

Mun gano cewa angon da tsohuwar budurwar ’ya’yan wa da kanwa ne kuma a gidan su angon ta tashi. Sai dai daga baya an ce ta danganta lamarin da aljannu tare da yin nadamar abin da ta yi.“

kunji yanda shafin suka ruwaitu Kuci gaba da kasancewa da shafin KuryaLoded domin samun zafafan labaram hausa dana Kannywood akan kayi mungode da ziyartarmu dakunkayi kufutta lafiya

Source:ArewTimes.com.ng

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *