Kukalli Wannan Matashin Da Yakaseh Mahaifansa Sabida Sunyi Batanci Ga Fiyayyen Halinta Anni Muhammad S A W

Posted by

Wani matashi mai suna Munkaila Muhammad Mazaunin ƙaramar hukumar Gagarawa dake jihar Jigawa ya kashe iyayen sa, ya kuma bayyana dalilin kashe su da cewa saboda sunyi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAWA.

 

 

 

Matashin wanda ya kasance mawaƙi kuma mabayin ɗariƙar Tijjaniyya, yace iyayen sa suna sukar sa da kiran sa mahaukaci, sannan suna inkarin wakokin sa da yake yi na yabon Manzon Allah.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda yan sanda suka kama matashin mai shekaru 37 bayan ya kashe iyayen sa sannan ya raunata wasu mutane 2 a ranar Alhamis.

Ya yi amfani da taɓarya wajen kashe mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, wanda shi ne Sarkin kauyen Zarada da ke yankin karamar hukumar Gagarawa, da mahaifiyarsa Hauwa’u, mai shekara 60.

A wani faifan bidiyo da aka nada a hannun ‘yan sanda da suka aikewa PREMIUM TIMES, Munkaila ya ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba domin an umarce shi da ya yi hakan.

“Na kashe su ne saboda sun ki yarda da gaskiya game da Annabi Muhammad (S. A.W.A). Na kashe su ne saboda zagin Annabi kuma hukuncinsu kisa ne, babu tuba ga duk wanda ya zagi Annabi.

“Ni mawakin yabo ne ga Annabi, bana nake niyyar yin bidiyon waka ta kuma in sha Allahu zan yi haka, zan samu ‘yanci na za a  sake ni, domin Allah yana tare da mai gaskiya, shi ya sa ban damu ba akan matakin da na ɗauka” in ji Munkaila a wani faifan bidiyo da ‘yan sandan suka dauka.

“Iyayena (ba sa son Annabi Muhammad) saboda ina girmama shi, sun kira ni mahaukaci, na roki mahaifina ya tallafa min akan aikin da nake yi (wakar yabo), kuma na ce masa ba na neman mata bana caca, bana shan miyagun ƙwayoyi, kuma ba na yin sata, amma ya ƙi.

“Mahaifiyata takan je garuruwan da ke makwabtaka da ni domin ta bata min suna, tana gaya wa mutane su ƙi ni a duk lokacin da na zo wakar yabon Annabi saboda mahaukaci ne ni kuma na ki yin aikin noma a gona.

“Yanzu ina hannun ‘yan sanda saboda a tunanin dan Adam na yi abin da bai dace ba, amma a wurin Allah da Annabi abin da na yi shi ne daidai,” in ji Munkaila.

Munkaila, wanda yake da ‘ya’ya biyar, ya ƙara da cewa yana zargin mahaifinsa da yin lalata da matarsa.

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *