Masha Allah Jami’an Tsaro Sun Samu Nasarar Kama Wani Matashi Daya Kashe Budurwar

Posted by

Yadda Jami’an tsaro sukayi nasarar kama wani matashi mai kimanin shekaru 23, da daya hallaka budurwar sa, har lahira sakamakon wayar salula.

Matashin da ake zargi mai suna Godspower Andessi, mai shekaru 23, yayi wa marigayiyar kutse kuma ya sareta da adda a wuya ta hanyar hallaka ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Brenda Erase, wanda ya tabbatar mana da faruwar wannan lamarin a wata sanarwa a ranar Lahadi, data gabata yace anyi nasarar kama matashin da ake zargin.

Wanda A cewar Brenda, wanda ake zargin ya kashe Gift ne bayan data 6ata wayar IPhone dinsa a lokacin da suke fada sakamakon wata matsala irin ta masoya.

“Wannan shine Godspower Adegheji na Etevie quarters Ozoro, mai shekaru 23, ya kashe budurwarsa Gift Oloku ‘f’ mai shekaru 22 a ozoro.

Ta hanyar amfani da adda bayan da tayi kuskure ta karya IPhone 11pro max din sa yayin da suke fada saboda ta fita ba tare da ta fada masa ba.

An kama shi.” Kakakin ya bayyana cewa zasuyi iyaka bakin kokarin su, domin ganin sun baiwa wannan yarinya hakkin ta akan abinda ya faru ita da saurayin nata.

Haka zalika iyayen yarinyar sun Kara maka matashin a wata babbar kotu ta ozoro mai no:23 domin ganin an yankewa matashin hukuncin k’isa ta hanyar data dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *