Matsalar Tsaro Ta’addanci Bai Hana Noma Ba A Najeriya ~Inji Ministan Noman Najeriya.

Posted by

Matsalar Tsaro Ta’addanci Bai Hana Noma Ba A Najeriya ~Inji Ministan Noman Najeriya.

Ministan Ayyukan Noma a Najeriya Mohammed Abubakar ya ce, ayyukan ta’addancin da kasar ke fuskanta ba su shafi ayyukan noma da samar da abinci ba.

A rahoton wanda gidan talabijin na Channels TV ya wallafa Ministan ya amince da cewa rashin tsaro ya na hana manoma shiga gonakinsu, musamman a yankin Arewa wanda hakan abin damuwa ne ga gwamnatin tarayya.

Ya ce, duk da haka, ana ci gaba da samar da abinci ba tare da wata matsala ba a wasu sassan yankunan kasar.

Ministan ya ci gaba da bayyana cewa, an samar da ayyuka kai tsaye daga kudin tallafin harkar noma na dala biliyan 1.1 da kasashen waje suka ba Najeriyar.

A cewarsa, Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya amince da ba da tallafin dala miliyan 538 domin a samar da shiyyoyin sarrafa noma na musamman a Najeriya. Bankin ya baiwa jihohin da suka halarci taron kamar su Akwa Ibom, Bauchi, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Kebbi, Ogun, Ondo, Oyo, Plateau da Sokoto. Ministan ya kuma karyata rahota

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *