Ni Ba Jahila bace na Hardace Al-qur’ani Maigirman tun daga Fatiha har Nasi, babu inda za’a ja mani ban ida ba” Inji Safara’u.
Kamar yadda matashiyar mawakiyar da ke tashe wato, Safara’u ta Wallafa a shafinta na Dandalin facebook, ta bayyana wasu muhimman zantuttuka dangane da kasuwancin da ta ke yi na rawa da waka kamar haka:
“Ni mahardaciyar Alƙur’ani hizif 60 ce, tun daga baƙara har nasi babu inda za kuyi min jaa ban kama na wuce ba Alƙur’ani hizif 60 ne cif cif a kai na”.
“Don kun ga ina sana’ar rawa da waƙa hakan baya nuna cewa ni jahila ce ko kuma Allah baya sona wallahi na tabbatar yana sona”.
“Saboda ya bani abinda mafi yawan masu zagi da aibata ni suna nema amma basu samu ba, kuma gaba ɗaya a cikin littafin Allah da hadusan MANZON ALLAH SAW babu inda aka haramta yin sana’a ni rawa da waƙa sune jari na”.
RELATED POSTS: Andaki Safarau Da Mr 442 Sunsha Daqyar A Wajen Wasan Da Sukayi