KANNYWOOD

Shin Kokunsan Soyayyar Dake Tsakanin Isa Ali Fantami da Jaruma Hadiza Gabon

Allahu akbar, Hotunan Jaruma Hadiza Gabon da Minista Farfesa Isa Ali Fantami sun yi taratsi a kafafen sada zumunta a Najeriya da sauran sassan duniya inda alakar da ake zarginsu da ita ta soyayya ce.

Jama’a da dama sun afka haumahauma da rumi domin ganin wannan hoton na yawo, lokacin da wasu suke ganin hadin bai dace ba, wasu kuwa suna ganin ai soyayya babu inda ba ta shiga.

 

Janzakitv ta yi nazari da zurfafa bincike da bin diddigin wadannan hotuna domin tantance sahihancinsu da bankado gaskiyarsu.

Hakazalika mun kuduri aniyar fallasa gaskiyar abinda bincikenmu ya gano mana komin dacinta ga mabiya wannan shafi namu na janzakitv.

Da farko dai Minista kuma farfesa Isa Ali Fantami shahararren malamin addinin Islama ne, mai hannu da shuni, sannann kuma matashi, ga ilimin boko domin kuwa har ya kure bokon da matakin Farfesa.

A dayan hannun kuma Jaruma Aliyu Gabon ‘yat Asalin Kasar Gabon ce, wanda sana’ar shirya fina-finan Hausa na Kannywood ya kawota Najeriya kuma Allah ya tarfa ma garinta nono, dan kuwa ta samu karbuwa a wajen jama’a inda ta kere sauran jaruman mata gaba daya da ta taras a kannywood din.

Binciken da muka gudanar akan wannan hoton dake sama wanda ya kunshi ita Jaruma Hadiza Gabon din da Ministan ba hoton gaskiya bane, amma ma’abucin janzakitv kada kayi mamaki domin za mu faiyace maka da hujjoji ingantattu.

Asalin hoton na Shehin Malamin kuma Minista Fantami ya dauke shi ne tare da Shugaban EFCC a wani lokaci a baya, auna tsaye kamar yadda hoton dake kasa ke nunawa.

Ita kuma nata hoton wani hoto ne na daban da aka samu wasu kwararrun tada zaune tsaye suka sarrafa hotunan biyu suka samar da shi wannan guda dayan sa ya ke ta yawo a kafafen sada zumun domin biyan wasu bukatunsu.

Yadda kuwa abin yake mai sauki ne, kowa na zai iya. Idan ka dauko shi hoton farko na Shehin malamin sai ka kaishi googleremovebackgroun.com sai ka cire backgroauund dinsa, ka aje a gefe, hakazalika hoto na biyun. Sai ka samo sabon background ka daura su duka hotuna biyun ka daidaita su.

Jama’a, janzakitv bata goyi bayan wannan danyan aika-aika ba, sannan tana kira ga masu irin wannan halin domin neman maziyarta wato traffic a kafafensu ko YouTube ko Website da su kiyayi fuahin Allah, su guji hada abubuwa na karya musamman shiga mutuncin masu mutunci, don ko ba komai Allah yana nan.

A karshe Kuryaloaded  na son jin ra’ayoyinku, shin ya kuke ganin wannan hadin, idan da Shi Ministan zai amince ita ma din ta amince ita ma Jarumar ta amince, hadin zai bada ma’ana?

Sai mun ji Ra’ayoyinku.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please