- Advertisement -

Tohfa Duba Yadda Aka Kama Rikakken Mai Garkuwa Da Mutane Tare Da Wasu Mabiyan Sa

Posted by

Dakarun Jami’an tsaron ‘yan sanda dake jihar Benue kudancin kasar nigeria, sunyi nasarar kama wani rikekken, dan ta’adda daya damu yankin jihar ta Benue.

- Advertisement -

A wayewar yau litinin akayi nasarar Kama Rikakken Mai Garkuwa Da Mutane Tare Da Yaransa, a yankin jihar Benue, sakamakon gudanar da wani bincike da hukumar ‘yan sandan yankin take gudanarwa a jihar.

Mutumin mai suna Samuel Achoho tare da yaransa sun jima suna addabar sassan jihar Benue da wasu yankunan jihohin dake makwabtaka dasu, domin ganin sun tashi al’ummar yankunan nasu.

Saidai kuma kamar yadda kuke gani mutumin mai suna semueal, din tare da yaran sa, anyi nasarar kama sune a yayin neman yunkurin awun gaba da wasu, mutane matafiya a yankin jihar ta Benue,

- Advertisement -

Wannan lamari yayi matukar baiwa Al’ummar yankin dake zaune a jihar tsoro sakamakon mutanan sun kasance suna cikin al’ummar yankin ana zaune tare dasu amma Ba’asan sana’ar da sukeyi ba.

Yanzu haka rundunar ‘yan sandan yankin tana kan gudanar da bincike akan wannan lamari domin tabbatar da gaskiya akan abinda mutanan suke aikatawa a yankin jihar ta Benue.

Kuci gaba da kasancewa da shafin ku Janzakitv, domin samun labaran duniya kowani lokaci mungode masoyan mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *