KANNYWOOD

Tohfa Kalli Yadda Aketa Zundumawa Rarara Zagi Kan Gasar Wakar Jagaba Shine Gaba Bayan Rigima Ta Kaure Da Wadanda Suka Shiga Gasar.

Tohfa Kalli Yadda Aketa Zundumawa Rarara Zagi Kan Gasar Wakar Jagaba Shine Gaba Bayan Rigima Ta Kaure Da Wadanda Suka Shiga Gasar.

Rarara Ya Bawa Mutane 6 Kyautar Motoci Ya Kuma Bawa Mutane 14 Kyautar Iphone 13 Pro Haka Zalika Ya Bawa Mutane 200 Kyautar Naira 100,000 Ga Kowanne Mutun Daya.

An dai yi bikin bayar da kyaututtukan ne ranar Asabar a babban dakin taro na ma’aikatar kula da kananan hukumomi watau Local Government Service Commission.

Taron ya samu halartar wasu kusoshin gwamnatin jihar Katsina da yan kwangila da ma ‘yan siyasa da suka hada da kwamishinonin kare muhalli da na harkokin watsa labarai da al’adu watau Honorable Hamza Suleiman Faskari da Hon. Abdulkareem Yahaya Sirika.

READ ALSO:  Jaruma Saima Muhammad Ta Sake Yin Aure

Sauran sun hada da dan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Katsina a karkashin jam’iyyar APC da dan takarar kujerar majalisar jiha mai wakiltar mazabar Kaita a jam’iyyar ta APC watau Hon Sani Danlami da Hon Surajo Kwaskwaro dai dai sauran su.

Haka zalika Katsina Post ta samu cewa fitaccen dan kwangilar nan na gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Sagir shima ya halarci taron da kuma yan fim da mawaka da ma wasu daruruwan masu ruwa da tsaki a harkar nishadantarwa da dama.

Chairman Alhaji Dauda Kahutu Rarara Ya Bawa Mutanen Da Sukayi Nasara a Gasar Daya Saka Ta Wakar Jagaba Shine Gaba Wadanda Sukayi Nasara a Tiktok Na Farko An Bashi Kyautar Mota Kirar Kamfanin Honda Continue Discussion Na Biyu An Bashi Kyautar Mota Kirar Honda EOD Na Uku Ma An Bashi Kyautar Mota Kirar Honda EOD Sauran Mutane Akwai Din Kuma An Basu Kyautar Waya IPHONE 13pro.

Haka Zalika Masu Normal Video Ma Na Farko An Bashi Kyautar Mota Kirar Kamfanin Honda Continue Discussion Na Biyu Ma An Bashi Kyautar Mota Kirar Kamfanin Honda Continue Discussion Na Uku Kuma An Bashi Kyauta Mota Kirar Kamfanin Honda EOD Sannan Kuma An Bawa Mutane Bakwai Kyautar Waya IPHONE 13pro.

Sannan Kuma Ya Bawa Mutane Dari Biyu Kyautar Naira Dubu Dari – Dari Ga Kowannen Su.

READ ALSO:  Asiri ya tonu kalli yadda murja Ibrahim yar tiktok take fadawa adam a zango wasu maganganu

Gadai Bidiyon Ku Kalla

Source:Arewanewseye.com.ng

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please