Wata kyakkyawar budurwa mai suna Ummi ta gamu da ajalinta a yayin harin da yan fashi da makami suka kai bankuna a jihar Kogi

Posted by


Wata kyakkyawar budurwa mai suna Ummi ta gamu da ajalinta a yayin harin da yan fashi da makami suka kai bankuna a jihar Kogi .

Marigayiya Ummi na tsaye kusa da daya daga cikin bankuna uku da aka farmaka lokacin da harbin bindiga ya zo ya same ta, nan take rai yayi halinsa.

A ranar Talata ne wasu yan bindiga suka farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu.

Kogi – Wata matashiyar budurwa mai suna Ummi ta rasa ranta a yayin farmakin da yan bindiga suka kai garin Ankpa, karamar hukumar Ankpa ta jihar Kogi a ranar Talata, 6 ga wata Satumba.

Wani da lamarin ya faru a idonsa ya ce harbin bindiga ne ya kashe matashiyar budurwar wacce ke kusa da daya daga cikin bankunan da aka yiwa fashin a wannan lokacin, shafin LIB ya rahoto.

An tattaro cewa kimanin makonni biyu da suka gabata ne marigayiyar ta kammala karatunta daga kwalejin Kimiyya ta Glory Land da ke Ankpa.

An rahoto cewa yan fashi da makamin fiye da 15 sun farmaki bankuna uku da misalin karfe 3:00 na ranar Talata, sannan suka yiwa bankunan da kwastamomi fashi.

Wata da ta san marigayiya Ummi mai suna Zuliahat Gold ta je shafinta na Facebook don nuna alhinin wannan rashi tare da wallafa hotunan marigayiyar.

Rundunar yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da harin

A halin da ake ciki, kakakin yan sandan jihar, SP William Ayah, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani jawabin manema labarai a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba.

A cewarsa, yan fashi da makamin sun farmaki bankuna uku a lokaci guda a garin Ankpa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Allah ya jikanta da Ramaha yasa aljance mako a gareta

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

Source:hausa.legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *