Yadda Wasu Marasa Tsoro Sun Yiwa Naziru Sarkin Waka Tatas Bayan Sakon Gardadi Da Ya Sake

Posted by

Majiyarmu tace kai al’amarin mutane sai su kawai abarsu da Allah domin duk wani nan wuya da zare ido ma mutum bafa zaisa mutane su dinga tsoran saba saboda Yanzu idon mutane a bude yake basa tsoran kowa sai kawa wanda Allah ya taimaka ake jin kunyarsa shine ba’a yi masa irin wa’yannan abubuwan da ake yiwa wanan mawakin wato Naziru Sarkin waka.

Mawakin ya fito media yajawa mutane musamman samari wanda suke hawa kan social media suna zaginsa inda yace daga yanzu sun daina dagawa kowa kafa zasu saka karar wanda daya gaduk wanda ya kara zaginsa domin yaga abin ya fara wuce gona da iri.

Sai dai kuma bayan yayi wannan maganar ba’a wani dauki lokaci sai gashi wasu daga cikin samarin wannan garin sun kara fitowa sunyi masa wankin babban bargo wanda suke nuna cewa ko meye zai faru ya faru kasancewar shima ai yana taba wasu acikin wannan Kafa ta sadarwa.

 

 

Allah ya shiryi domin a yanzu zuciyoyin mutane sun riga sun karkashe basa tsoro ko kuma jin kunyar kowa daga mutum ya nuna yanajin karfi ko kuma izza da fariya da wani abu to ananne wulakancin mutane yake tashi na nuna masa iyakarsa.

A wannan karan dai Sarkin waka baiji dadin wannan abinda aka kara maimaitawa akan saba domin yana ganin wannan abin da yayi bazaisa wasu su kara yi masa fitsara ba ashe ya tsokano tsuliyar dodo saboda Yanzu ma aka fara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *