Wata mata wacce muryarta ta dinga yawo a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok a kwanakin baya inda ‘yan mata su ka dinga hawa muryarta ta bayyana yadda ta ritsa mijinta da mata 8 akan gadon aurensu.
Kamar yadda bidiyon wanda shafin lucky udu ya wallafa a Facebook, an ji yadda matar take bayani dalla-dalla inda tace an samu wannan muryar tata ne a jawabin da tayi a kotu.
A cewarta, mijin nata baya aikin fari balle baki, sai shaye-shaye da bin mata, amma a wannan karon abinya ta’azzara don ta dawo daga tallar magungunar kwari ne ta ritsa shi da mata 8.
A cewarta, shigarta dakin ke da wuta ta ji sautinsa da na matan, sai ta karasa ciki taji yana canja matan yayin da ya ke lalata da dukansu kamar yana canja zannuwa.
A cewarta, mamaki ne ya kama ta hakan yasa ta nemi jin wannan ba’asin, sai ya gaura mata mari tare da ce mata kada ta dinga shiga harkokin da basu shafe ta.
Ta bayyana yadda ta tattara ya nata ya nata ta tafi gidan iyayenta tare da yaranta biyu wadanda dama ita ce take kulawa da su.
Sai daga bisani ta amsa gayyatar kotu inda alkali ta nemi jin ta bakinta bayan mijin ya kai kararta wanda ta shaida cewa mata 8 ta kama shi da su.
Anan ne alkalin ta nemi su shirya amma duk da haka abin ya ci tura. Ta ce yanzu haka ba sa tare kuma tana ci gaba da lallaba rayuwarta.
One comment