LABARAI

YANZU YANZUN Jami’ai Ankama Wani Matashi Yanayiwa Qanwarshi Fyade

Wani matashi mai suna Abubakar Hamidu, ya fada komar ’yan sanda a Jihar Gombe kan zargin yi wa kanwarsa fyade.

Matashin mai kimanin shekaru 35 da ke zaune a Unguwar Jauro Abare, ana zarginsa da yin lalata da ’yan uwar tasa har sau biyu a lokuta daban-daban.

Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya ce wani mai suna Muhammad Hamza ne ya shigar da karar matashin a ranar 19 ga watan Yulin da muke ciki.

Baba’ita ya ce mai shigar da karar wanda ke zaune a Unguwar Kasuwar Mata, ya kai wa ’yan sanda korafin cewa wanda ake zargin ya yi lalata da kanwar tasa ce karon farko a wani gida da ya zama kufai a Unguwar ta Jauro Abare.

Kwamishinan ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan, ASP Mahid Mu’azu, ya ce an sake kama matashin karo na biyu yana aikata masha’ar da kanwar tasa a bakin wani tafki.

A cewarsa, da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu domin ya fuskanci shari’a.

READ ALSO:  ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Jami’an Tsaro Da Mutanen Gari Masu Yawa A Jihar Katsina

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please