LABARAI

Yadda Wata Tsaleliyar Budurwa Me Tallen Pure Water Ta Koka Akan Yadda Samari ke Karban Number wayarta Maimakon Sayen ruwanta.

The business of selling plastic water called ‘Pure Water’ and synthetic water ‘Bottled Water’ and other types of lemons on the streets has become common around the world due to the acceptance of the business as a way to get money. and kobo for those who do it and help those traveling in vehicles and even on the ground when the need arises

Sana’ar sayar da ruwan leda da a ke kira da ‘Pure Water’ da ruwan roba ‘Bottled Water’ da nau’ikan lemuka a kan tituna ya zama ruwan dare gama duniya sakamakon karbuwa da sana’ar ta samu a matsayin hanyar samun taro da kobo ga masu yinta da kuma taimakawa masu zirga-zirga a ababen hawa da ma a kasa abin jika makoshi a lokacin da bukatar hakan ta kama.

Wata zukekiyar budurwa mai sayar da ruwa a Accra babban birnin kasar Ghana ta koka kan yadda maza ke tsayar da ita amma ba don su sayi ruwa ko lemon da ta ke talla ba, a’a, sai kawai don su karbi lambar wayarta da nufin su kirata bayan ta gama tallan don su fahimci juna.

Sai dai kuma wannan mai sai da ruwa ba wata bace illa fitacciyar mawakiyar kasar Ghana nan Nina Ricchie ta yi bad da kama a wani salo na yaki da munanan dabi’u a cikin al’umma, musamman ta’adar dora talla ga ‘yan mata

READ ALSO:  Dan Allah Dan Annabi Wani Yazo Ya Aure Ni, Sai Kace Bani Da Kyau- Wata Tsaleliyar Budurwa Ta Koka Tana Neman Mijin Aure Ruwa A Jallo

Nina ta dora a shafinta na Instagram yadda ta sha fama da samari a dan fita da ta yi talla na dan sa’o’i kadan, inda ta yi kokarin bayyanawa iyaye irin hadarin da ‘ya’ya mata suke fuskanta a lokacin da suka fita talla.

Sau tari ‘yan mata masu talla na karewa ne da tallata kansu a maimakon kayan da suka dauko talla

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please