LABARAI

Yin Nasarar ‘Yan Bindiga Na Kudirin Sace Buhari Da El-Rufa’i Shine Zai Kawo Karshen Matsalar Najeriya Inji Reno Omokri

Shahararren marubuci, kuma dan rajin kare hakkin bil’adama, Reno Omokri ne ya bayyana haka a wata wallafa a shafin sa na Tuwita.

Cikin wallafar da yayi a ranar lahadin nan, Omokri yace; Me yasa wadannan ‘yan fashin ke barazanar sace Buhari da El-Rufai? Ban tunanin ‘yan Najeriya sun dauki hakan a matsayin barazana. Ga ’yan Najeriya da dama, hakan zai zama abin annashuwa. Buhari wanda ya hau karagar mulki ya sami Dala tana ₦190 yau kuma ya kai ta ₦650. Sace shi tamkar sace matsalar Najeriya ne, inji Omokri.

Wannan bayani na Omokri na zuwa ne biyo bayan fitar wani bidiyo da ‘yan ta’addan da sukai garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja suka fitar, inda aka gano su suna dukan wadanda ke hannun. Yayin da a bangare guda suka ci alwashin sace shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

“Lokacin da El-Rufa’i yake biyan wadannan ‘yan fashi kudin fansa a shekarar 2016, mun gargade shi, amma bai ji ba. Yanzu kuma suna barazanar saceshi, shi da Buhari, yana yi musu gargaɗi, amma ba su saurara. Daga karshe, wadanda ke biyan ‘yan ta’adda suma sun bi layin waɗanda ake shirin sacewa.”

Kazalika, a wani bangare ya kara da cewa, kuna gani gwamnatin Buhari ta iya samun nasara na gano Nnamdi Kanu, mutum dake rayuwa a wuri mai nisan kilomita 5000 a kasar Kenya, amma me yasa suka kasa iya gano maboyar ‘yan ta’addan da aka gani cikin bidiyo suna dukan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna tare da horar da wadanda aka sace tare da yin barazanar sace Buhari da El-Rufai ba?

Ya ce; ‘Yan ta’adda yanzu su ke mulkan gwamnatin mu! Abin mamaki. Har ma sun ce farmaki na gaba Buhari za su sace. Ina Buhari da El-Rufai za su yi ritaya bayan 2023 su zauna lafiya? Kamar yadda ake yi, Buhari ba zai iya ko yin ritaya ya koma zuwa Kaduna ko Daura ba. Watakila dai zai bi matarsa, Aisha zuwa Dubai ne.

Mun gargadi Buhari a lokacin da yake ta kalamai ga ‘yan ta’adda. Yanzu ‘yan ta’adda sun juya suna gargadin Najeriya kamar yadda suke yiwa Buhari barazana.”

“Kada ku yaudari kanku; Allah ba a yi masa ba’a: iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girba.”—Galatiyawa 6:7, inji Omokri.

 

 

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please