Cikin Fushi Ali Nuhu Ya Yi Martani Ga Buhari Akan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

Posted by

Cikin Fushi Ali Nuhu Ya Yi Martani Ga Buhari Akan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya yi martani a kan sabon bidiyon da yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Abuja-Kaduna suka saki.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, Ali wanda aka fi sani da sarkin Kannywood ya nuna bacin ransa a kan yadda gwamnati ta zuba ido tana kallon yan ta’adda na cin karensu babu babbaka a kasar.

MASU ALAQA: Batareda Tsoro ba Jaruma Hadiza Gabon Tayiwa Buhari Allah Ya Isa Akan Bidiyon Zane Fasinjojin Jirgin Kasa

Daraktan fina-finan ya tambaya ko haka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta ci gaba da zuba ido ana azabtar da

al’ummanta ba tare da cika alkawarin da ta dauka na kare rayuka da dukiyoyin talaka ba.Hakazalika jarumin ya tambayi ina imanin shugabanni da ke rike da madafun iko, inda ya jaddada cewa hakkin al’umma a kansu ba karya bane.

MASU ALAQA: Video Yadda Masu Satan Mutane Ka Dukan Fasinjojin Jirgin Qasa

Daga karshe Ali ya roki Allah madaukakin sarki a kan ya kawowa bayinsa mafira a kan wannan hali da suka tsinci kansu.

MASU LAQA: Ali Nuhu Zai Angwance Da Wata Yarinya Budurwa Menene Gaskiya?

Ya rubuta a shafin nasa:

“Yanzu haka Gwamnatin zata zuba ido tana kallon al’umma da ta yi alkawarin kare rayu kansu da dukiyoyin su a cikin wannan hali? Ina imanin shugabanni? Hakkin al’umma akan ku fa ba karya bane.

[ads1]
“Allah ya kawo hanyar da mutanen nan zasu samu mafita, amin.”

Cikin Fushi Ali Nuhu Ya Yi Martani Ga Buhari Akan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

Ba Ali Nuhu Kadai ba, Wasu daga cikin jaruman kannywood da yawa Suna sun fito Sunyi Allah Wadai tareda yin tirr Akan wannan gwamnatin ta Buhari.

MASU ALAQA: Adam A zango Ali Nuhu da Laila sun koka kan Harin jirgin kasan kaduna

Falalu a Dorayi

Cikin Fushi Ali Nuhu Ya Yi Martani Ga Buhari Akan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

 

 

2 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *