Innalillahi Wa’inna IlaihinRaj’un Kull Nafsin Za’ikatil Maut Allah Yayiwa Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW Ya Rasu

Posted by

Mai gadin kabarin Manzon Allah SAW, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, Allah yayi masa rasuwa a yau Laraba.

Agha Habeeb Muhammad Al-Afari ya jima yana fama da jinya.

Ya yi aiki a matsayin babban mai kula da kabarin Annabi Muhammad SAW, tsawon Shekaru sama da 40.

Anyi jana’izarsa bayan Magriba a Masallacin Annabi SAW dake Madina, 13 ga watan Yuli, 2022.

Dakin da aka bizne Annabi Muhammad SAW ana kiransa dakin alfarma ko Rawdah Mubarak, kuma wurin ne aka bizne kalifofin Annabi Muhammad SAW na farko da na biyu, Sayyidina Abubakar (RA) da Sayyidina Umar (RA).

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *