Andaura Auren yar autar marigayya Jaruma Amina Garba Dumba

Posted by

Anyi Auren yar autar marigayya Jaruma Amina Garba Dumba

Allahu akbar tsohuwar jaruma a masana’antar kannywood wacce ta rasu dadadewa wato Hajiya Amina Garba Dumba anyi auran yar ta wacce itace yar auta acikin ya’yan da jarumar ta haifa a duniya kuma tayi aura sun tare tare da mijinta

Yarinyar da bata wuce shekara ashirin ba itace yar kara wacce jarumar ta mutu ta bari a duniya wanda lokacin da ta rasu tana karama nata iya mallakar hankalinsuba sai gashi cikin ikon Allah yanzu ta zama amarya acikin sabuwar Shekarar nan

An daiga manyan jarumai mata da maza a wajen taron bikin musamman ma matan na kannywood wanda sune sukayi uwa kuma sukayi makarbiya acikin sha’anin bikin kuma angansu suna chashewa wanda hakan ba karamin sha’awa ya bawa mutane ba

 

 

Ganin karar da jaruman kannywood din sukayiwa marigayyar yasa mutane suke ta yabonsu domin koda tana raye itakacin abinda zasuyi kenan sai gashi dukda bata Nan sunyi abin a yaba musu

Sai dai kuma kash mutane daba’a iya musu saida suka soki jaruman inda sukace ai su jaruman inda sabga ce ta biki tofa anan sukafi karfi inda za’a ga suna rawar jiki dakai mari wajen anyi komai dasu saboda shagalarsu

Amma kuma abinda mutane basu duba ba shine yariyar fa da akayiwa bikin yar tsohuwar jarumar wasan kwaikwayo ce aiki bakomai sayi kara wajen halattar bikin Allah ya jikan mahaifiyar ta da rahama ya kuma bata zaman lafiya agidanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *