KANNYWOOD

Hakikanin Gaskiya Akan Jirgin sama (Private Jet) Da Akecewa Ali Nuhu Ya siya

Gaskiyar magana kan jirgin saman da Ali Nuhu ya siya

Jarumin wasan kwaikwayo kuma jigo a masana’antar kannywood wato Ali Nuhu an dai ga bidiyo da kuma hotunansa sun cika gari cewa yasiyo jirgin sama

Sai dai hakan ba gaskiya bane cewar jarumi Ali Nuhu sai dai yace komai lokacine idan Allah yayi zai siya amma dai yanzu bashi da halin dazai siyi jirginsa

Ali Nuhu yace jama’a basa raboda zancen kanzan kurege yace yadda kowa yaji ya gani shima haka yaji kuma yaga wannan zance na cewa ya siyo jirgin sama

A cikin bidiyon yayi kira ga jama’a su daina yadda da kowanne zance indai basu tantanceba domin watarana za akaisu a baro

To amma wasu sunce ai wannan fatan alkhairi ne da ake yi masa me yasa ba kowa akace ya siyo jirgiba sai shi kasan cewar kawai ya shiga cikin zukatan Al’umma ne kawai

Ali Nuhu dai yace shima tsintar labarin yayi kawai yana yawo a gari hakan yasa yayi bidiyo domin ya sanar da jama’a gaskiyar wannan magana yace fatan dai jama’a zasu gamsu da cewa bafa gaskiya bane cewar ya siyo jirgi

Sai dai kuma ya godewa masu yi masa fatan alkhari da kuma jinjina musu bisa nuna kauna da kishi da suke nunawa akansa Allah ya bar zumunci
 

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please