Dantakarar Shugaban Kasa A Jam’iyar PDP Atiku Ya Mayar Da Martani Kan Daukar Shettima A Matsayin Mataimakin Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya mayar martani kan daukar tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na APC Bola Ahmed Tinubu.
Atiku a cikin sanarwar da ya fitar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yu watsi da harkar siyasar nuna wariya, inda ya kara da cewa, Nijeriya a baya ta fuskanci irin wannan harkar siyasar ta nuna wariya.
Wazirin na Adamawa ya kuma bukaci ‘yan kasar da su yi watsi da harkar siyasa irin ta nuna ra’ayin da bai dace ba, musamman idan aka yi la’akari da irin yanayin da Nijeriya ta ke a ciki a yau.
Atiku ya ci gaba da cewa, a mulkin da APC ta yi a shekaru bakwai da suka wuce ya gaza tabukawa ‘yan Nijeriya wani abun azo a gani, inda ya yi nuni da cewa al’umma, na ci gaba ne kawai idan ana damawa da kowa.
A cewarsa, “Tafiyar da muka faro mun yi ta ne don kai Nijeriya ga tudun mun tsira, inda ya yi nuni da cewa, tafiyar da APC ta zo da ita domin cin zabe a cikin sauki aba ce ta sabawa harkar siyasar kasar nan.”
- RELATED POST: Ga Yadda Zaka Cike Sabon tallafin bashi daga Nirsal Microfinace
- RELATED POST: Innalillahi wa’inanna ilaihi raji’un Gobara ta halaka mata da miji likitoci Allah Kamasu Rahama Amin
One comment