Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raj’un Kalli Yanda Samari Ke Lalata Da ‘Yan Mata Da Sunan Soyayya

Posted by

Yanzun Nan mukasamu wani Rubutu a Kafar Sadarda Zumunta Ta Facebook Inda Marubucin Ya Bayyana yanda yaran zamanin Nan ke Qoqarin Mayarda Duk Wata Budurwa Mazinaciya Da Sunan Suna Soyayya.

kada na cikakaku da surutu ga rubutun nan akasa saiku karanta sannan kumana Share da comments na ra’ayoyinku mungode da kulawarku

Mazan Zamani Da Bautar Sha’awa

Daga Ahmad Nagudu

Wato na fahimci mazan zamanin nan idan aka bar su fa, so su ke su mayar da duka mata mazinata a kaikaice da sunan Soyayya.

Saboda daga yadda mu ka ɗauki sha’awa da bauta mata, tamkar ibadar Sallah haka abun akwai tashin hankali a cikin sa. Babu dama ƳA MACE ta yi rayuwar ta lami lafiya, ba tare da wani namiji ya nemi shiga ciki ya gurbata ta ba. A wannan zamanin duk kamun kai da nutsuwar mace, ba ta kuɓuta daga farmakin maza masu bautar sha’awa. Ko a suna ko a hoto ko a giftawa ko a murya, in dai mace ce, to, sai maza sun yi mata ca ko da ba su taɓa gan ta ba. Kuma a cikin kaso 100 da ƙyar ka samu kaso 10 da ke harin ta da zimmar aure ko wata harka ta kirki. Kowa kawai da zarar ya isa in da ta ke, zancen dai ɗaya ne, “To, ya za a yi ne?”

Ƙarshe zancen dai kawai, neman haɗin kan ta a ke yi don a samu damar kebewa a biya buƙata da ita. Fakat!

Wato akwai maza da yawa da su na rayuwa a cikin mutane ne, amma TSINANNU ne tuburan wallahi. Domin in dai mace za ta ba su haɗin kai, wani ko uwar sa ne zai iya jinginar da ita ko ya sayar da gidan gado don ya yi amfani da kudin don neman biyan buƙatar sha’awar sa a wajen yaudarar kowace irin mace ce da azzakarin sa ya kaɗa a kan ta.

Allah Ya sawwaƙe mana, Ya kuma raba matan kirki da irin waɗannan la’anannun lalatattun mazan.

domin samun ire iren wadannan rubutun toh dinga ziyartar wanna shafin namu na KuryaLoded.ng Mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *