Kalli Biidyon Chasun Wasu Daga Cikin Matan Kannywood a Wajen birthday Party din jaruma samira Ahmad

Posted by

Wasu daga Cikin Sha Hararrun Jarumai Mata Na  kannywood suka chashe a bikin birthday din jaruma Samira Ahmad

Tsohuwar jaruma Samira Ahmad tayi bikin karin shekaru wato birthday kuma ta tara jaruman kannywood mata gaba dayan su sun hallaci wajen bikin birthday din ya dauki hankali ganin yadda jaruman masana’antar kannywoodkannywood suka cika inda kowace tazo da ya’yan ta

[ads1]

Anga hotunan birthday na jarumar inda aka ganta tare da ya’yan ta da kuma yan uwanta ga kuma jarumai mata na kannywood sunyi cikar dango

 

 

Samira Ahmad jaruma ce wacce tayi yayi a shekarun baya sannan daga bisani kuma tayi aure inda ake ganin har yanzu tana dakin mijin nata

An bayyana ta acikin jarumai masu kamun kai wacce ake ganin bata tabayin abin kunya ba har tabar masana’antar tayi aure kuma a halin yanzu ma tana da kanwa acikin kannywood mai suna Asiya Ahmad

Kuma itace jarumar da bata dade tana film ba kuma tayi suna sosai inda wasu ke cewa kawai domin tana da kyau ne matuka

Amma wasu agefe na ganin wannan rashin da’a ne ace mace da auranta amma tana tara matan film akan bikin birthday duk da ta kasance tayi aure be halatta ba koda kuwa da yardar mijin inda wasu kance ya kamata tasan cewa itafa yanzu ba kamar yan film takeba

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *