Kotu ta daure wani matashi bayan karuwa ta mutu su na tsaka da lalata

Posted by

Kotu ta daure wani matashi bayan karuwa ta mutu su na tsaka da lalata

Wata kotun majistare da ke Akure a Jihar Ondo ta umarci a daure wani Dele Ebenezer, mai shekaru 31 bisa zarginsa da zama sanadiyyar mutuwar wata karuwa, LIB ta ruwaito. Dan sanda mai gabatar da kara, Omhenimhen Augustine ya sanar da kotu cewa ana zarginsa da halaka Blessing Eze mai shekaru 47, sanadiyyar lalatar da yayi da ita.

Augustine ta bayyana yadda mamaciyar ta shiga mawuyacin yanayi yayin da su ke tsaka da lalatar wacce ta yi sanadin mutuwarta. Ana zarginsa da aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Yunin 2022, da misalin karfe 4 na safiya a Otal din Cool Corner cikin Ondo, sai dai bai amsa laifin ba. A cewarsa Augustine, laifin ya ci karo da sashi na 316(2) kuma hukuncinsa na karkashin sashi na 319 na dokar Criminal Code Cap 37. Volume 1, na dokokin Jihar Ondo, 2006. Lauyan wanda ake zargi,

C.O Falana ya bukaci kotu ta ba shi damar yin rantsuwa. Alkalin kotun, O. R Yakubu ya bukaci a sakaya wanda ake zargin a magarkamar ‘yan sanda sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Yulin 2022. Na so ace ana kai ziyara lahira, Matashin da budurwarsa ta rasu ana gab da aurensu Abdulmuhyi Bagel Garba, kanin kwamishinan wutar lantarki da kimiyya da fasaha na Jihar Bauchi,

Hon Garba Bagel, ya yi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta mai taba zuciya bayan watanni 6 da rasuwar budurwarsa, LIB ta ruwaito. LabarunHausa ta ruwaito yadda Hauwa Abdullahi Shehu, dalibar aji uku a jami’ar Jihar Bauchi, Gadau ta rasu sakamakon hadarin motar da ta yi ana saura wata daya ayi aurensu. Abdul, wanda dan sanda ne yana shirin auren Hauwa a Azare, Jihar Bauchi a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairun 2022, sai mutuwa tayi musu yankan kauna.

A ranar Asabar 2 ga watan Yuli, Abdulmuhyi yayi wata wallafa a shafinsa na Instagram inda yace: “Naso ace ana zuwa lahira ziyara da na bukaci ganinki don sanar da ke yadda rayuwata ta kasance babu ke, Allah ya gafarta miki masoyiya. “Amma watarana, radadin yana nunkuwa fiye da na ranar da lamarin ya faru.

Allah ya sanya yi a Aljannar Firdaus.” Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Related Posts

Yadda Hotunan Wani Magidanci Bahaushe Tareda Iyalansa Ya Janyo Cece-Kuce a Kafar Sada Zumunta

Related Posts 

Bazan Iya Daina Harkar Fim ba Dukda Cewar Nayi Aure Yanzu Cewar Rahama Mk Dalilin…

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *