Wataa Sabuwar Rigima Ta Barke Tsakanin Malam Ali Kwana Casain Na Rayya Inda Sukayi Ta Kundumawa Juna Munanan Ashar

Posted by

Wata sabuwar Rigima Ta Barke Tsakanin Malam Ali Kwana Casain Na Rayya Inda Sukayi Ta Kundumawa Juna Munanan Ashar

Wani video da ya fara yawo a dandalin tiktok ya nuna Jarumin shirin kwana 90 Abdul saheer wanda aka fi sani da Malam Ali a shirin yana Iullukawa Rayya ta shirin ashariya ta uwa ta uba ba tare da an san musabbabin wannan tarzoma ba

Sai dai ana iya jin malam alin yana korafin ya zo wurin aiki bashi da lafiya an fita da shi ranga ranga ya dawo ba wanda yayi masa sannu sai ma cewa aka yi wai an kula da shi

Bayannan an sake jin wani sautin murya inda Malam Alin ya aikawa da rayya ashariya dai kwando kwando ta manhajar Whatsapp inda ita ma ta mayar

kamar yadda zakuga cikakken bidiyan anan

 

 

Kawo iyanzu dai bamu san makasudin wannan balahira ba da har ta kai ga aunawa iyeyen juna kwandon ashariya sai dai muna fatan Allah ya huci zuciya ya kuma yayyafa mata ruwan sanyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *