’Yan Bindiga Sun Farmaki Sansanin Sojoji A Dutsen Zuma Da Ke Dab Da Abuja

Posted by

An shiga zulumi da yammacin ranar Alhamis, bayan wasu da ake zargin ‘yan tada kayar baya na Boko Haram ne suka kai hari kan wani shingen sojoji da ke kusa da dutsen Zuma a jihar Neja.

Yankin yana kusa da garin Madalla a jihar, wanda ke da dan nisan ’yan mintuna daga Zuba a Abuja, a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wata majiya a yankin da ta zanta da Aminiya a daren nan, ta ce maharan sun kai harin me bayan karfe bakwai na dare, kuma sun kai kusan tsawon minti 30 suna harbe-harbe, kafin daga bisani suka bi hanyar Kaduna bayan sun gama cin karensu ba babbaka.

Kazalika, wata majiya ta kara da cewa, bayan tafiyar maharan da kamar minti 20 sai wasu dakarun sojoji suka fito daga barikin soji na Zuma mai tazarar kilomita kadan, inda suka isa wurin tare da ‘yan sandan.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken rahoto kan lamarin, amma ana fargabar maharan sun kashe sojoji da dama da suka samu a wajen.

A baya-bayan nan an samu rahoton cewar ‘yan ta’adda na shirin kai hari kan wuraren ibada, makarantu da sauransu wurare.

Lamarin da ya tilasta rufe makarantun Firamare da Sakandare da ke Babban Birnin Tarayyar da kuma jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *