LABARAI

Fati Muhammad Ta Jawo Cece Kuce A Kafar Sadarwa Tare Maganganu Kan Talata Atiku Abubakar

Jaruma fati Muhammad ta haddasa cece kuce a dandalin Twitter sakamakon taltata dan takarar shugabancin kasa Atiku Abubakar a dandalin Twitter inda ma’abota dandalin Musamman yan kudu ke mata martani da suka kalakala kan tallata dan takarar gami da sukar ra’ayin ta

Sanin kowa ne Dandalin cike yake da dandazon yan kudu wandu wanda mafi akasari su suka mamaye) kafar kana yan takarkarun shugabancin kasarnan kafatanin su babu wayanda ke samun goyon bayan yan kudun kamar dan takar jam’iyyar wato Peter Obi kasancewar sa dan kudun da ya dauki mataimakimusulmi dan arewa
Sabanin sauran yan takarar da basu cika sharuddan da suka yi daidai da ra’ayin yan kudun ba inda kwankwaso ya kasance dan arewa dukda ya dauko abokin takara pastor bai rasa samun suka daga yan kudun ba kana Atiku shimadai kasancewar sa dan arewa yasa wasu yan kudun ke sukar sa duk da – kasancewar shima abokin takarar sa dan kudun ne kuma kirista

A yayin da bola tinubu shi kuma duk da kasancewar sa dan kudun daukar abokin takara musulmi ya zamar masa kalubake kásancewar suna adawa da tiktin musulmi da musulmi wato musuli shugaba mataimakin sa ma musulmi bayaga kuma saba yarjejeniyar da suke ganin an yi na musulmi daga arewa ya shekara 8 yana mulki ya kamata mulki ya koma kudun kuma hannun kirista wanda aka fi ganin daukacin yan kadun na goyon bayan peter a shafukan sada zumunta musamman musamman a dandalin Twitter

Sai dai kuma wannan kashi mu raba da aka yiwa Al’ummar Nigeria a zaben na bana jama’a da dama da masu nazari kan al’amuran siyasar na kyautata zaton Nasara ga Atiku Abubakar dan takarar Jam’iyyar pdp duba da shinea jam’iyya mafingirma da kuma ke da saukin kalubale daga masu suka- kana shiyyar da ya fito ta aréwa tafi rinjaye da yawan A’umma

Jaruma Fati Muhammada wacce ta dadé tana gwagwarmayar neman zaben Atikun tun a kakar zaben da ta wuce wannan karon ma ta fito da karfin ta in da take ta kokarin hado kan Jarumai kamar yadda ta saba da wakoki da sauran shirye shirve na kamfen din jagoran na iam’iyyar pdp

A irin wannan kokari nata tayi wata wallafa a dandalin twitter da ya ja cece kuceinda ma’abota dandalin musamman yan kudu ke ta yi mata martani inda ta wallafa hotunan ta guda hudu uku tana tsaye daya tana zaune inda ta rubuta i stan with atiku ma’ana na tsava da Atiku

Anyi ta yi mata martani inda wasu ke cewa gajiya tayi da tsayuwarshiyasa ta zauna a hoton karshe? wasu ko na inda wasu ko na kokarin bayyana gazawa ko laifukan atikun a sanda ya zama mataimakim shugaban kasa wasu-ko na kokarin bashi kariya inda aka barke da mahawara a shafin jarumar daga nan Fati ta cigaba da wallafa abubuwa da suka shafi dan takarar nata gami da martani ga masu kalubalantar ta musamman mabiya Peter Obi

kamar yadda ta fara wallafa ‘Hi Ystday I pated Smthing Some pple are cmmentng Peter Obi All the way.While Me,I don’t even know who’s peter Obi, pls am askg a question?,who is da Peter Obi, is he Contesting.7 An evn if he’s contesting wat is he contesting for? ls he contosting for chairman or councilor.

Jarumar bata tsaya anan ba sai ta kara da wallafa wata magana kamar haka‘Peter Obi can only win elections on l twitter simply because his supporters have knowledge of twitter forgetting that elections happens in polling unit Not in Twitter page.Pater Obi Campaing Fund

wannan maganar da jarumar ta wallafa tare da hotunan atiku yayi matukar tada tarzuma a kafar sadarwa inda akayi ta cecec kucen magana da fatan Allah ya bawa nijeiriya shugaba na gari da zai kare martaba talakawansa.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please