KANNYWOOD
Masha Allah Yanzun Maryam Booth Tabayyana Wanda Zata Aura
Jarumar Kannywood, Maryam Booth ta hau shafinta na Instagram domin yada hotunan Mijinta (Ango).
Hotunan da ta saka ya sa masoyanta su ka yi ta maganganu a shafukan sada zumunta musamman na arewacin Najeriya.
Jaruma Maryam Booth ta yi matukar farin ciki da a karshe ta bayyana fuskar angonta ga masoyanta a shafukan sada zumunta.
Ta Buga Hoton tare da Takaitaccen bayanin hoton da ke cewa; Mrs Yusuf. a ƙasa ma’ana amaryar Mallam Yusuf da Hausa.
Hotunan dai ya jawo martani da dama daga masoyanta a shafinta na Instagram, yawancinsu sun yi mata murna sosai kuma suna taya ta murna yayin da take shirin shiga wani babi na rayuwarta.
Credit: Maryam Booth/Instagram.
Ga kadan daga wasu maganganu daga magoya bayanta a cikin hoton da ke ƙasa.