KANNYWOOD

Sabuwar rigima na shirin Barkewa a kannywood tsakanin rahama sadau dakuma Mansura Isah

RAHAMA Sadau ta mayar wa furodusa Mansurah Isah da martani kan taƙaddamar su dangane da sunayen jaruman Kannywood mata da aka zaɓa don taya Bola Ahmed Tinubu yaƙin neman zama shugaban ƙasa.

Mujallar Fim ta labarta maku jiya cewa da Rahama ta ga sunan ta a jerin sunayen, ta fito ta ce babu ruwan ta da su, domin ba ta san yadda aka yi aka saka ta a ciki ba.

Ita kuma Mansurah sai ta fito ta faɗa wa Rahama cewa da ma can ba sunan ta aka yi niyyar sakawa ba, kuskuren rubutu ne.

A raddin da ta yi a yau, Rahama ta faɗa wa Mansurah cewa na sama da ita Mansurar ma sun kira ta sun ba ta haƙuri ta bayan fage. Ta ce mata, “Zuwa ga Mansura Isa, ina ba ki shawarar ki bar abin nan ya wuce saboda magabatan ki sun kira ni ‘a cikin sirri’ don neman afuwa kan ‘kuskuren da aka yi da gangan’. Ba sai kin ari bakin wani kin ci masa albasa ba. Sai anjima.”

Waɗansu sun kalli wannan martanin na jarumar ta Kannywood da Nollywood a matsayin yarfa wa Mansurah magana ta yi, daidai da irin maganar da ita ma ta yi wa Rahama ɗin.

Mujallar Fim ta tambayi Rahama Sadau a ɓangaren sharhi cewa, “Ba dai faɗa ba ne ko?” Sai ta amsa da cewa, “Ban tabbatar ba, amma yanayin maganar ta ne bai dace ba.”

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su, wasu na zuga, wasu kuma na ba da haƙuri.

A nata ɓangaren, Mansurah ba ta sake komawa kan maganar ba har zuwa yanzu.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please