Yanda Aminu Alan Waka Ya shafe Shekara 7 Yana Rubuta Wakar Yabon Ma aiki Annabi (Muhammad SAW)

Posted by

Fitaccen Makin Hausa Aminuddeen Ladan Abubakar, wanda ake masa lakabi da Alan Waƙa, ya bayyana cewa ya shafe shekara dai-dai har 7 yana rubuta wakar da yaya wa Manzon Allah SAW; ya kara da cewa ya saka wa wakar suna; Muhammadu miftahul futuhati linzamin rayuwata

Ya kuma kara da cewa ya kwashe shekarun ne kafin ya kammala rubuta waƙar saboda sai da ya gudanar da bincike, inda ya ƙara da cewa waƙar ta shafi tarihin rayuwar Annabi Muhammad (S A W) tun daga haihuwa har zuwa wafatin sa dan haka dole sai an tsaya a nutsu wajen wannan waka.

“Irin wannan babban aiki yana matukar bukatar bincike na tarihi da kuma irin kalmomin da za’a yi su akan Fiyayyen Halitta, samun matsala kuma shi yaban ma’aiki kaman ka zuba karkashi a kasa ne a koda yaushe zaka iya zamewa.

Hakazalika yace ita waka “Mufitahul futuhati” littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana inda ya kuma ce babu shakka mutane sun ji dadin wakar “kuma nima Ina alfahari da ita.

Ya ce mafiyawan wakokinsa yana gina sune kan Ilimi kuma yana gudanar da bincike kafin yayi kowacce waka, inda ya ce “domin yin hakan shi yake bani damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka.

Daga karshe dai ya shawarci mawaka da su ringa bincike kafin siyi wakar yaban ma’aiki Sabida kada garin samun lada ka dauki alhaki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *